Ɗan wasan gaban Nijeriya, Victor Osimhen, ya kafa sabon tarihi a gasar zakarun Turai bayan zura ƙwallaye uku a ragar Ajax yayin da ƙungiyarsa ta Galatasaray ta samu nasara a wasan mako na huɗu.
Wannan nasarar ta sa Osimhen ya zama ɗan wasan Nijeriya da ya fi kowane zura ƙwallaye a gasar zakarun Turai, inda yake da jimillar ƙwallaye 25, ya doke tsohon tauraron Nijeriya Obafemi Martins wanda ke da ƙasa da hakan a tarihin gasar.
- Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro
- Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Osimhen, wanda ya ci ƙwallaye shida a bana a gasar zakarun Turai, ya zarce manyan ’yan wasa kamar Harry Kane, Kylian Mbappe, da Erling Haaland, waɗanda kowannensu ke da ƙwallaye biyar.
Rashin nasarar Ajax ya sa ta ci gaba da zama a ƙasan teburin gasar, bayan ta sha kashi a dukkanin wasanninta huɗu.
Galatasaray kuwa ta tana maki tara, inda ta ke daf da shiga jerin ƙungiyoyin saman teburi da ke neman zuwa zagaye na gaba.
Osimhen, wanda ya koma Galatasaray daga Napoli, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya, ciki har da lashe kofin ƙalubale.
A yanzu haka, shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Galatasaray ƙwallaye a dukkanin da ta ke bugawa a bana, ya bar sauran fitattun ’yan wasa irin su Leroy Sane da Mauro Icardi a baya.














