Dan wasan gaba na Super Eagles dan kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta kasar Italiya, Victor Osimhen, ya samu kyautar gwarzon matashin dan wasa a kyautar ‘Globe Soccer Award’ ta 2022.
Tsohon dan wasan gaban Lille na Faransa ya doke Gavi da Valverde a wurin samun kyautar a wani bikin da aka gudanar a Madinat Jumeirah a Dubai a watan Nuwamba 2022.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Osimhen ya ce yanzu haka ya karbi kyautar da ya lashe watanni biyu da suka wuce inda ya nuna kyautar shi a wani hoton da doka tare da ita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp