Fadar shugaban kasa ta ce mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, bai yi wani hatsari ba a safiyar yau Litinin.
Kakakin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Osinbajo ya gamu da hatsarin ne da ya faru a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama Sai ya tsayar da ayarinsa domin taimakawa wadanda abin ya shafa.
Ya ce, “Mataimakin shugaban kasa Osinbajo na kan hanyarsa ta zuwa Owo, jihar Ondo, Sai ya hadu da mummunan hatsari akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Abuja.
“Nan da nan ya dakatar da ayarin motocinsa, ya kuma bukaci motar daukar marasa lafiya da ta kai wadanda lamarin ya rutsa da su asibiti sannan kuma ya bukaci akai masa rahoton halin da wadanda hadarin ya rutsa da su.
“Daga bisani kuma, ya wuce filin jirgin don hawa jirginsa zuwa Akure.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp