Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta karbi lambar yabo karo na biyu daga kungiyar Peace Ambassadors Network ta Nijeriya (PAN) sakamakon ficen da ta yu wajen kulawa da Walwalar Mata Da Marayu.
Hajiya Huriyya ta karbi lambar yabon a wurin taron da ya gudana a cibiyar kungiyar samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice da ke Abuja.
Mataimakiya ta musamman a kan yada labarai ta matar gwamnan, Zahara’u Musa ce ta bayyana haka a takardar da ta aike wa LEADERSHIP Hausa a Gusau.
A cewar sabarwar, uwargidan gwamnan, Huriyya Lawal, ta bayyana godiya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma wadanda suka shirya taron da suka karrama ta a cikin wasu fitattun ‘yan Nijeriya masu matukar daraja da kima.
“Na yi farin ciki da jin dadi matuka bisa girmama ni da kuka yi da kuma kasancewa cikin wadanda suka ci gajiyar wadannan kyaututtuka.
“Zaɓa ta cikin waɗanda aka ba wannan Lambar karramawa a matsayi mace mafi tsayuwa ga lamurran mata kan sha’anin daidaiton jinsi abun jinjina ne da godiya matuka.
“Na gode muku kwarai da gaske da kuka amince da irin gudunmurwar da muke bayarwa kan sha’anin mata da yara.”, in ji ta.
Hajiya Huriyya Lawal ta kuma bayyana mijinta Dauda Lawal a matsayin Jigo da ma’aunin dukkan nasarorin da ta samu.
A karshe Hajiya Huriya Dauda ta sadaukar da kyautar karramawar ga al’ummar Jihar Zamfara baki daya.