Jamiyyar PDP reshen jihar Zamfara ta zargi Bello Mohammed Matawalle kan kitsa murde sakamakon zaben mahaifar sa ta karamar hukumar Maradun da ke jihar.
PDP ta ce, Bello ya tuntubi wasu daga cikin manyan jami’an hukumar INEC don a murde sakamakon zaben karamar hukumar Maradun.
A cikin sanarwar da PDP ta fitar da safiyar yau litinin a garin Gusau tq hanyar ofishin yada labaran ta wacce Dauda Lawal ya fitar, Bello bai shirya
amincewa da sakamakon zaben gwamna da aka yi a ranar asabar ba.
Sanarwar ta ce, Bello na tunanin hakan zai yi masa sauki wajen murde sakamakon zaben karamar hukumar Maradun, inda sanarwar ta ce, tuni INEC ta sauke sakamakon zaben na mazabu 185 daga cikin jimlar mazabu
195 na karamar hukumar Maradun.
Sanarwar ta ce, APC tq samu kuri’u 26,170 inda PDP ta samu kuri’u 12,543
Sanarwar ta kara da cewa, ratar daga mazabu 185 sun kai 13,627.
Sanarwar ta ce, Bello ya bukaci jimi’an INEC da su kara akalla kuri’u 50,000 kafin a sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Maradun, inda sanarwar ta ce, dole ne INEC ta zame kanta daga cikin shirin da Bello ya kitsa.