Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar PDP ya amince da jadawalin taron shiyoyi na 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa za a zabi sabbin mambobin kwamitocin gudanarwa na shiyoyi da kuma shugabannin na shiyoyi a wannan babban taro.
- Janar Gowon: Tsohon Shugaban Kasa Mafi Tsawon Rai A Nijeriya Na Cika Shekara 90
- Babu Hannun Mijina A Wahalar Da Ƴan Nijeriya Ke Sha
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa ya amince da gudanar da taron shiyoyin.
Ya bayyana cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya amince da jadawalin a yayin taronta na 592, gabanin karewar wa’adin shugabannin shiyoyin na Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Arewa-maso Gabas.
Sanarwar ta bayyana jadawalin ayyuka, ta ce, “Sayar da fom ga dukkan mukaman na sabbi da tsofaffin shugabannin shiyoyi na kasa a Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas: Litinin, 18 ga Nuwamban 2024 zuwa ranar Laraba, 18 ga Disamban 2024.
“Wa’adin karshe na miyar da fom din takara zai kasance a ranar Juma’a, 17 ga Janairun 2025.
“Tantance ‘yan takara a hedikwatar shiyya, zai kasance ranar Asabar, 25 ga Janairu, 2025.
“Amincewa da tantance ‘yan takara a hedkwatar shiyya, zai kasance ranar Asabar, 1 ga Fabrairu, 2025.
“Wallafa sunayen ‘yan takara, zai kasance ranar Laraba, 12 ga Fabrairun 2025. Buga jerin sunayen wakilai, zai kasance ranar Alhamis, 13 ga Fabrairun 2025.
“Ranakun babban taron shiyoyin na Arewa maso Gabas, Kudu maso Gabas, da Kudu maso Kudu, zai kasance ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025.
“Amincewa da babban taron shiyoyin, zai kasance ranar Talata, 25 ga Fabrairu, 2025.
“Babban taron shiyoyi na shiyyar Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yamma, zai gudana a ranar Asabar, 22 ga Maris, 2025. Amincewa da babban taron, zai kasance ranar Laraba, 26 ga Maris, 2025.”
Jam’iyyar ta bukaci duk masu son yin takara da su tuntubi sakatariyar jam’iyyar na kasa don samun bayanai kan kudaden da ake bukata da sauran tambayoyi.
Ologunagba ya kuma ja hankalin dukkan shugabannin PDP da masu ruwa da tsaki, da ’ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da hada kan su, su kuma yi kokarin ganin jam’iyyar ta samu ci gaba.