Jam’iyyar PDP ta bai wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wa’adin sa’o’i 48 da ya fayyace kalaman da aka ce shi ya yi akan dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, in ba haka ba, Jam’iyyar itama za ta fallasa shi.
Jam’iyyar PDP ta yi barazanar fadawa ‘yan Nijeriya da ma duniya baki daya wanene Obasanjo a zahiri.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibrin, ya bayyana cewa shi da jam’iyyar PDP suna matukar mutunta tsohon shugaban kasar.
Jibrin ya kara da cewa, furucin zai zama abin takaici matuka idan furucin da aka alakanta ga Obasanjo wanda ya karade kusan dukkan jaridun Nijeriya ya Tabbata daga bakinsa ne.
Ya bayyana kalaman Obasanjo na cewa “ya yi kuskure wajen nada Atiku abokin takararsa” abin damuwa da takaici ne matuka.