A safiyar yau Juma’a ne mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping madam Peng Liyuan da masu dakin shugabannin kasashen Kyrgyzstan da Uzbekistan wadanda ke halartar taron koli a birnin Xi’an, suka ziyarci gidan wasan Guyi wato cibiyar nuna al’adun gargajiya na lardin Shaanxi na kasar Sin.
Da farko madam Peng ta ziyarci dakin adana kayayyakin fasahohin wasan Qinqiang na kasar Sin tare da manyan bakin, inda suka saurari asalin tarihin ci gaban wasan Qinqiang, kuma sun yi gwajin fasahar samar da kayayyakin wasan kwaikwayon ‘yar tsana ko shadow play a dakin nune-nune na Guyi Agency.
Daga baya sun je gidan wasan kwaiwayo mai tsawon tarihin shekaru 100 domin kallon wasan Qinqiang, inda Peng Liyuan ta bayyana cewa, muna son kara karfafa cudanya da kasashen tsakiyar Asiya a bangaren fasahohin al’adu, ta yadda za a kara zurfafa zumunta dake tsakanin al’ummomin kasashen baki daya. (Mai fassarawa: Jamila)