A yau ranar 1 ga watan Satumba da yamma, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matan shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO masu halartar taron kolin SCO na shekarar 2025 sun ziyarci kogin Haihe na birnin Tianjin tare.
Peng Liyuan da sauran matan shugabannin sun hau jirgin ruwa tare da sauraran tarihin birnin Tianjin da yadda ya bunkasa. Peng Liyuan ta bayyana cewa, birnin Tianjin birni ne da ya hade dogon tarihi da zamani, kana kogin Haihe ya kasance tare da bunkasar birnin Tianjin da kuma al’adu daban daban, tana fatan za su ji dadi a yayin ziyarar. Dukkan bakin sun yaba da al’adun gargajiya masu kyau na kasar Sin, da kuma nasarorin da aka samu kan zamanantarwa irin na kasar Sin. (Zainab Zhang)














