Da safiyar ranar 6 ga wannan wata, agogon Faransa, uwar gidan shugaban kasar Sin kuma wakilyar musamman ta UNESCO kan ingiza ba da ilmi ga yara ‘yan mata da mata Peng Liyuan, ta ziyarci hedkwatar hukumar dake Paris bisa gayyata.
Yayin da ta yi ganawa da babbar jami’ar hukumar Audrey Azoulay, Peng Liyuan ta yi kasaitaccen bayani kan sabon ci gaban da kasar Sin ta samu wajen ingiza ba da ilmi ga yara ‘yan mata da mata, inda ta bayyana cewa, ba da ilmi ga yara ‘yan mata da mata babban aiki ne dake shafar ci gaban bil Adama. Don haka a shirye kasar Sin take ta yi kokari tare da UNESCO domin kara zuba jari kan aikin, ta yadda za a samar da karin damammakin samun ilmi ga mata.
A nata bangare, Audrey Azoulay ta bayyana cewa, UNESCO ita ma tana son kara karfafa hadin gwiwa da cudanya da kasar Sin domin sa kaimi ga aikin. (Mai fassara: Jamila).