Mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, wato uwar gida Peng Liyuan, da babbar daraktar hukumar raya ilimi, kimiyya, da Al’adu ta MDD UNESCO, uwargida Audrey Azoulay, sun halarci bikin mika lambobin yabo a fannin raya ilimin yara mata da mata na hukumar UNESCO na shekarar bana, da kuma bikin cika shekaru 10 da fara gudanar da mika lambobin yabon, a jiya Juma’a a nan birnin Beijing.
Yayin bikin, uwar gida Peng, wadda ita ce jakadiyar musamman ta UNESCO a fannin ingiza ci gaban ilimin yara mata da mata, da Azoulay, sun mika lambobin yabo ga wakilan wasu shirye-shiryen da suka yi fice daga kasashen Kenya da Lebanon.
A jawabin da ta gabatar, Peng ta ce cikin sama da shekaru 10, wadanda aka karrama da lambobin yabo daga sassan kasa da kasa, da mutane masu hangen nesa daga sassan duniya daban daban, sun taimakawa yara mata da mata, wajen dacewa da damammakin bunkasa zamantakewar al’umma, da cimma nasarorin raya kai ta hanyar samun ilimi.
Ta ce a halin yanzu, al’ummar dan Adam na shiga wani sabon zamani na basira, don haka yana da muhimmanci a mayar da hankali sosai ga ilimin kimiyya domin mata, da taimakawa karin mata wajen samun ilimin kimiyya, da koyon dabarun amfani da sabbin fasahohi, da inganta ikonsu na kirkire-kirkire.
Peng ta kara da cewa, har kullum kasar Sin na dora muhimmancin gaske ga ingiza ilimin kimiyya tsakanin mata, da fatan ganin an zurfafa hadin gwiwa da UNESCO, da sauran sassa masu ruwa da tsaki wajen karfafa sanin makamar aiki a fannin raya ilimin kimiyya ga mata, da hada hannu wajen daga matsayin ilimin kimiyya ga mata.
Ta ce tun bayan da Sin da UNESCO suka kafa wannan dandali na gabatar da lambobin yabo a fannin raya ilimin yara mata da mata a shekarar 2015, kawo yanzu, a mika jimillar irin wadannan lambobi 20 ga ayyuka daban daban da suka cancanta daga kasashe 19. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp