Yanzu haka shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, yana ziyarar aiki a kasar Sin tare da mai dakinsa. Da yammacin jiya Talata, mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping Madam Peng Liyuan, ta zanta tare da shan shayi tare da mai dakin shugaban na Equatorial Guinea, Madam Constancia Mangue de Obiang, a birnin Beiijng, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin tattaunawar ta su, Madam Peng Liyuan ta yi matukar jinjinawa ayyukan tallafawa jama’a mabukata da Madam Constancia ta yi, ta hanyar goyawa mata baya wajen gudanarwa, da raya sana’o’insu, kuma a tsawon lokaci da ya gabata, Madam Constancia ta dukufa wajen raya harkokin ba da ilmi, da kiwon lafiya da sauransu.
- Majalisar Dattawa Ta Amince Da Dokar Dawo Da Tsohon Taken Kasa
- Yunkurin Sarrafa Batun Yankin Taiwan A WHA Zai Ci Tura
Madam Peng ta kara da cewa, ana fatan kasar Sin da Equatorial Guinea, za su kara bunkasa mu’amala da hadin kai, domin kare hakkin mata, da raya harkokin ilimi da kiwon lafiya da hadin gwiwa, don samar da alfanu ga al’ummun kasashen biyu.
A nata bangare kuwa, Madam Constancia Mangue de Obiang, jinjinawa kasar Sin, da ma Madam Peng Liyuan ta yi, don gane da kulawar da suke baiwa yara, da matan Equatorial Guinea, da ma sauran kasashen nahiyar Afirka, tare da gudummawar da suka bayar a fannin kiwon lafiya, da wadatar da jama’a. Ta ce, kasarta na fatan karfafa mu’amala, da hadin gwiwar dake akwai tsakaninta da kasar Sin, gami da zurfafa zumunci a tsakaninsu kamar yadda ake fata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)