Mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta ziyarci babban gidan adana kayan tarihi na kasar Sin tare da uwargidan shugaban kasar Philippine Louise Araneta-Marcos. Uwargida Louise Araneta-Marcos ta rako mai gidan ta shugaba Ferdinand Romualdez Marcos Jr. ne a ziyarar aikin sa a kasar Sin.
Yayin da suke ziyartar gidan adana kayan tarihin a jiya Laraba, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta ce Sin da Philippines makwafta ne na kusa, dake kuma fuskantar juna daga tsallaken teku, kuma Philippine muhimmiyar kasa ce dake kan hanyar siliki ta teku.
Peng ta kara da cewa, fatan ta shi ne al’ummun kasashen biyu, su ci gaba da inganta kawancen gargajiya, da daga matsayin alakar su zuwa sabon mataki.
Ita kuwa a nata tsokacin, Louise Araneta-Marcos godewa Peng ta yi, bisa gayyatar da ta yi mata zuwa babban gidan adana kayan tarihi na Sin, ta kuma bayyana fatan ziyarar za ta ba ta damar inganta, da zurfafa fahimtar tarihi da al’adun kasar Sin. Ta ce ya kamata al’ummun kasashen biyu, su ci gaba da ingiza ruhin hanyar siliki, da bunkasa amincewa da juna da abotar dake tsakanin su. (Saminu Alhassan)