Kocin Manchester City Pep Guardiola ya rattaba hannu kan tsawaita kwantiragin shekara daya, tare da zabin karin shekara guda, wanda zai iya ci gaba da rike shi har zuwa shekarar 2027, Guardiola ya taka rawar gani a tsawon lokacin da ya shafe a Etihad ya samu nasarar lashe kofunan gasar Firimiya sau hudu a jere wanda shi ne karo na farko da wani ya yi haka a tarihin kwallon kafa ta Ingila.
Labarin ya samu karbuwa sosai daga magoya baya da kuma masana harkar kwallon kafa, wadanda ke kallonsa a matsayin wani shiri na ci gaba da jagoranci a Manchester City,a karkashin jagorancin Guardiola kulob din ya samu gagarumar nasara a gida da waje,kamar nasarar cin kofin zakarun Turai a shekarar 2023.
Tsawaita zaman Guardiola ya sake tabbatar da aniyar Manchester City na yin aiki kafada da kafada da manyan mashawarta a harkar kwallon kafa wajen ganin ta cigaba da jan zarenta a harkar kwallon,wanda hakan ke kara tabbatar da su na amsa sunansu na matsayin babbar kungiyar kwallon kafa a duniya.