Shugaban jam’iyyar Labour Party (LP), Barista Julius Abure, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar, Mista Peter Obi, ba shi da wani shiri na fice wa daga jam’iyyar.
A cewar Abure, tattaunawa da ke ci gaba da gudana a tsakanin Peter Obi, Atiku Abubakar da kuma Rabiu Musa Kwankwaso kawai ta ta’allaka ne a kan yadda jama’a za su mara wa ‘yan takaransu baya su samu nasara a zaben 2023.
- Jam’iyyar LP Ta Obi Na Shirin Kulla Auren Siyasa Da NNPP Ta Kwankwaso —Dakta Tanko
- 2023: Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar LP, Pat Utomi Ya Janyewa Peter Obi
Da yake magana a taron manema labarai a bikin ranar demokradiyya ranar Litinin, Abure ya kara da cewa Obi da jam’iyyar Labour sun maida hankali ne kan yadda za su tafi da matasa domin gina Nijeriya.
Muddin Obi ya zama Shugaban Kasa a Nijeriya, kasar nan za ta samu tagomashi da damar gudanar da rayuwa mai cike da inganci, “Tabbas idan Obi ya zama Shugaban Kasa tabbas zai taka gagarumar rawa wajen bunkasa kasar nan, kan haka ne jam’iyyar mu ta fito da shi a matsayin dan takara domin ya fuskanci babban zaben 2023.”
“Idan har Peter Obi da Labour Party suka samu nasara, tabbas kalubalen da ke fuskantar Nijeriya za su zama tarihi,” don haka ne ya jawo hankalin ‘yan Nijeriya da su nemi karin jefa kuri’a su adana domin zabin Labour Party a zaben 2023 domin ceto Nijeriya daga halin kakanikayi da ake ciki a yau