Sojojin kasar Sin sun kori jirgin ruwan yakin Amurka na Higgins, da ya kutsa yankin tekun kasar Sin ba bisa ka’ida ba a kusa da Huangyan Dao a yau Laraba, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin kasar ya bayyana.
Jami’in, He Tiecheng, wanda yake mai magana da yawun rundunar sojojin ruwa ta PLA a shiyyar kudancin kasar Sin, ya bayyana cewa, rundunar shiyyar ta shirya wasu dakaru ta hanyar bin doka, domin su bi diddigi, da sanya ido, da yin gargadi, da kuma korar jirgin ruwan yakin na Amurka, wanda ya shiga yankin ruwa dake kusa da Huangyan Dao ba tare da izinin gwamnatin kasar Sin ba.
Matakin na Amurka ya yi matukar keta hurumin kasar Sin da tsaronta, ya kuma kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, kana ya saba wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin da suka shafi dangantakar kasa da kasa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp