ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

by Abubakar Abba and Sulaiman
10 months ago
Manja

Kungiyar Masu Shuke-shuken Kayan Lambu ta Kasa (POFON) ta bayyana cewa, tana bukatar karin hekta 500,000, domin noman kwakwar manja.

Har ila yau, ta sanar da cewa; tana da wannan bukata ce, domin kara bunkasa noman kwakwar manjan tare da samar da wadatuwarta, duba da karin bukatar da ake da ita a fadin kasar baki-daya.

  • NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai
  • Ana Ci Gaba Da Caccakar El-rufai Kan Kalamansa Game Da Tsaron Kasa

Shugaban kungiyar na kasa, Mista Emmanuel Ibru, ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi, kan batun yadda kungiyar za ta samar da wadatacciyar kwakwar manjan a Nijeriya da kuma batun daidata farashinta a daukacin fadin kasar.

ADVERTISEMENT

Shugaban ya bayyana cewa, kungiyar za kuma ta daidai ta farashin kwakwar, har zuwa karshen shekarara; hatta a cikin kowace kakar noma a kasar.

“A daukacin Nahiyar Afirka, Nijeriya ce kan gaba wajen noman kwakwar manja, sannan kuma ita ce ta biyar a noman kwakwar manjan a dukkanin fadin duniya,” in ji Ibru.

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana

Ya kara da cewa, saboda haka; akwai bukatar a kara yawan hektar noman kwakwar manjar zuwa hekta akalla 500,000, domin cike gibin bukatar da ake da ita a kasar nan tare kuma da kara bunkasa nomanta a Nijeriya baki-daya.

Shugaban ya ci gaba da cewa, har yanzu a Nijeriya ana ci gaba da fuskantar samun gibi wajen samar da kwakwar, sai dai ya bayyana cewa; sama da shekara 10 zuwa shekara 15 kungiyar ta POFON ta yi namijin kokari, wajen kara yawan noman kwakwar a daukacin fadin kasar.

A cewarsa, manyan gonaki a kasar da ke nomanta kamar irin su, Presco da kuma Okomu sun kara dage damtse wajen zuba hannun jari da kuma kara fadada gonakin noman kwakwar manjan kwarai da gaske.

Haka zalika, shugaban ya bayyana cewa; wasu sabbin gonaki kamar irin su Dufil, Saro Africa da sauransu, sun shiga Jihar Edo tare da zuba hannun jari a fannin na noman kwakwar.

“Saro Africa, ta samar da hekta 20,000 a Jihar Edo, Wilmar ta mallaki hektar noman kwakwar ta PZ Wilmar, inda yanzu yake kokarin sake noma wasu hektocin guda 8,500, wanda hakan zai bai wa gonar damar hekta guda 50,000 a cikin kasar.

“Gonakin JB, su ma sun kara zuba hannun jarinsu a Jihar Kuros Ribas, inda a yanzu suke kan kara samar da wasu hekta guda 10,000, ta noman kwakwar manjan a Jihar Ondo,” a cewar shugaban.

Ya ci gaba da cewa, akwai kuma wata gonar ta noman kwakwar manjan da ke ci gaba da kara zuba hannun jarinsu.

“Kimanin shekaru takwas da suka gabata, jimillar gundarin manjan da ake samarwa a kasar, a wannan yankin ake samar da shi wanda ya kai daga tan 900,000 zuwa tan miliyan daya,“ in ji shugaban.

“Ya zuwa yanzu, mun samu nasarar kara yawansa zuwa kimanin daga miliyan 1.4 zuwa miliyan 1.5, wanda hakan ya nuna cewa; ya kai kashi 50 na manjan da aka sarrafa,” in ji Ibru.

Koda-yake dai, shugaban ya sanar da cewa; ana ci gaba da samun gibi a samar da kwakwar manjan a kasar, amma kungiyar na kan yin aiki da wasu hukumomin gwamnati, domin samar da wani jadawalin kara bunkasa fannin a kasar nan da kuma kara zuba kudi a bangaren.

Ya yi nuni da cewa, jadawalin, ba wai kawai manyan masu noman kwakwar manjan ba ne, hatta su ma kananan monoma a fannin, za su yi matukar amfana.

Da yake yin tsokaci kan tsadar manjan a fadin wannan kasa, Ibru ya bayyana cewa; kungiyar na ci gaba da yin kokari wajen daidaita farashinsa kwarai da gaske.

“A wannan kasa da muke ciki, sau biyu ake yin noman kwakwar manja a shekara, yadda idan aka girbe ta da yawa, farashin nata ke raguwa daga baya kuma farashin ya kara tashi,“ a cewar shugaban.

Haka zalika, ya sanar da cewa; ‘ya’yan kungiyarmu na matukar kokari wajen ganin sun daidata farashin manjan a fadin kasar baki-daya.

Manja
Abubakar Abba
+ posts Bio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    “Mutunta Ƴancin Addinai Ita Ce Hanyar Wanzar Da Zaman Lafiya A Kaduna”
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Ɗaura Ɗamarar Magance Matsalolin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana
Manja
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia
  • Sulaiman
    “Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka
  • Sulaiman
    Shugaba Xi Ya Gana Da Firaministan Koriya Ta Arewa A Beijing
  • Sulaiman
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu

MASU ALAKA

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu
Noma Da Kiwo

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

July 4, 2026
Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana
Noma Da Kiwo

Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana

July 3, 2026
Manoma Sun Nemi Tinubu Ya Kara Yawan Tallafin Noma 
Noma Da Kiwo

Ko Shirin Da Gwamnatin Jihar Katsina Ke Yi Wa Manoma Zai  Amfane Su A wannan Daminar?

June 27, 2026
Next Post
Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

LABARAI MASU NASABA

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?

July 10, 2026
“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Sana’ar Ɗinki: Yadda Telolin Zariya Suka Yi Fice A Sassan Afirka

July 10, 2026
Shugaba Xi Ya Gana Da Firaministan Koriya Ta Arewa A Beijing

Shugaba Xi Ya Gana Da Firaministan Koriya Ta Arewa A Beijing

July 10, 2026
Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira

Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira

July 10, 2026
Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga A Wani Ƙauyen Katsina

Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga A Wani Ƙauyen Katsina

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ibrahim Aliyu Na Ci Gaba Da Rasa Tasiri A Harkar Fili Da Gidaje A Yankin Abuja

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Fafutukar Neman Sabon Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.