Alkalumman hukuma sun nuna Litinin din nan cewa, an samu bunkasuwar yanayin kasuwanci a fannin masana’antu na kasar Sin a watan Yuli, yayin da muhimman alkaluman suka karu a cikin watanni biyu a jere.
A cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin, alkaluma a fannin sayayyar hajoji (PMI) na sashen ya kai kashi 49.3 cikin 100 a watan Yuli, kana alkaluman na PMI da bai shafi bangaren masana’antu ba ya kai kashi 51.5 ciki 100 a watan Yuli. Kasuwancin masana’antu da wanda bai shafi bangaren na masana’antu ba, duka sun kasance cikin yanayi na daidaito, a hannu guda kuma tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da farfadowa. (Mai fassara: Ibrahim)