Dan wasan tsakiya da ke buga kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke buga gasar Serie A ta kasar Italiya, Paul Pogba, ya yanke shawarar daukaka kara a kan hukuncin da wata kotu ta yanke masa na dakatarwa daga harkar kwallon kafa na tsawon shekaru 4.
“Na ji bakin cikin jin wannan hukuncin da aka yanke a kaina na dakatarwa saboda nasan ban taba shan wani abu na kara kuzari da ya sabawa doka ba,” cewar Pogba.
Talla
Pogba wanda ya taba zama dan kwallon da yafi kowane tsada a lokacin da Manchester United ta saye shi daga hannun Juventus, ya kasa tsallake wani gwajin amfani da kwayoyi masu kara kuzari da aka yi masa a watan jiya.
Talla