Paris St-Germain ta dauki dan wasan gaban Portugal Goncalo Ramos daga Benfica a matsayin aro.
Dan wasan mai shekaru 22 ya ci wa Portugal kwallaye uku a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a bara, kuma ya ja hankalin manyan kungiyoyin Turai da dama.
Ya zura kwallaye 27 a wasanni 47 da ya buga wa Benfica a kakar 2022-23.
Zuwan Ramos ya zo ne a daidai lokacin da jaridar L’Equipe ta bayyana Neymar ya shaidawa shugaban PSG Nasser Al-Khelaifi cewa yana son barin kungiyar.
Wannan labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kwantiragin da kungiyar ta kulla da dan wasan gaba Kylian Mbappe ke kwarewa.
Ramos shi ne babban dan wasa na tara da kulob din ya saya a bana.
PSG na da zabin siyan dan wasan gaban a karshen zaman aronsa, kwatankwacin yarjejeniyar da Mbappe ya zo kungiyar daga Monaco a 2017.
Tuni dai PSG ta sayi gola Arnau Tenas da ‘yan wasan baya Milan Skriniar da Lucas Hernandez da ‘yan wasan tsakiya Marco Asensio da Manuel Ugarte da Lee Kang-in da Xavi Simons da kuma Hugo Ekitike.