Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta shiga gaban takwararta ta kasar Ingila, Chelsea wajen neman daukar dan wasan gaban Nijeriya mai buga kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Napoli Victor Osimhen a kakar wasa mai zuwa.
PSG ta nuna shaawar daukar gwarzon dan kwallon na Afirika akan zunzurutun kudi har yuro miliyan 120 a kakar wasa mai zuwa daga Napoli.
- Barcelona Ta Kai Matakin Kwata Final A Gasar Zakarun Turai Bayan Shekara 4
- Chelsea Za Ta Fafata Da Real Madrid Da Manchester City A Amurka
Tattaunawa tsakanin PSG da Napoli akan daukar Osimhen tayi nisa sosai yanzu haka a kokarin da zakarun na Faransa keyi wajen ganin tsohon dan kwallon na Lille ya koma babban birnin Paris domin cigaba da taka leda kamar yadda jaridar II Mattino ta ruwaito.
Tun da farko dai Chelsea ce ta nuna shaawar daukar Osimhen domin ta kara karfafa yan wasan gabanta bayan da Piere Emerick Aubameyang ya koma Olympique Marseille a bara.