Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea za ta fafata wasannin sada zumunta da Manchester City da kuma Real Madrid a kasar Amurka a wasannin shirin tunkarar kakar badi ta 2024 zuwa 2025. Kawo yanzu dai Chelsea tana ta 11 a teburin Premier League da maki 39, wadda saura wasanni 11 ya rage mata a kakar nan a gasar firimiya ta Ingila wanda za a iya cewa kakar wasa ce wadda magoya bayan kungiyar ba za su taba mantawa da ita ba saboda rashin kokari.
Sauran wasan da kungiyar ta Chelsea za ta fafata a Amurka har da wasa da kungiyar Wredham da Celtic da kuma Club America duka a kokarin kungiyar na ganin ta koma kan ganiyarta a kakar wasa mai zuwa. Chelsea mai buga gasar Premier League za ta yi tata burza da Manchester City ranar Asabar 3 ga watan Agusta sannan za kuma ta kece raini da Celtic a college football arens wato a Ohio Stadium a Columbus a birnin Ohio.
- Azumi Lokaci Zafi: Yadda ‘Yan Kasuwar Kankara Ke Camamarsu A Yobe Da Zamfara
- Rundunar ‘Yansandan Bauchi Ta Fara Cafko Masu Garkuwa Ta Amfani Da Fasahar Zamani
Ranar Talata 6 ga watan Agusta, Chelsea za ta fuskanci Real Madrid a Bank of America Stadium, Char-lotte a Carolina – filin da ta buga wasa a shekarar 2015 da kuma 2022. Jerin wasannin da Chelsea za ta buga a Amurka Chelsea da Wredham – Laraba 24 ga Yuli a Lebi Stadium a Santa Clara, Chelsea da Celtic – Asabar 27 ga Yuli a Notre Dame Stadium, Notre Dame, Indiana.
Chelsea da Club America – Laraba 31 ga Juli a Mercedes-Benz Stadium a Atlanta, Georgia. Chelsea da Manchester City – Asabar 3 ga August a Ohio Stadium a Columbus, Ohio. Wasan da aka fafata a bayan nan tsakanin Chelsea da Manchester City.
Kakar wasa ta 2023 zuwa 2024
Premier League Asabar 17 ga watan Fabrairun 2024 Man City 1 – 1 Chelsea Premier League Lahadi 12 ga watan Nuwambar 2023 Chelsea 4 – 4 Man City Chelsea da Real Madrid – Talata 6 ga Agusta a Bank of America Stadium, Charlotte, Aewacin Carolina. Wasan da Chelsea da Real Madrid suka kara a baya bayan nan Champions League Talata 18 ga watan Afirilun 2023.
Chelsea 0 – 2 Real Madrid Champions League Laraba 12 ga watan Afirilun We 2023 Real Madrid 2 – 0 Chelsea Wasan Chelsea da Man City daya ne daga tsarin gurmurzu tsakanin fitattun kungiyoyin tamaula da aka shirya mai suna 2024 FC Series. Haka kuma Chelsea da Real Madrid za su kece raini a daya daga gumurzun Soccer Champions Tour da ake yi tsakanin manyan kungiyoyi da ake buga a Amurka.
Filayen da Chelsea za ta buga wasa a Amurka
Filin wasa da ke Ohio mai dumbin tarihi zai bai wa magoya bayan Chelsea damar ganin ‘yan wasa da shirin da take na tunkarar kakar wasa ta badi – wadda kaka ta biyu kenan da ba za ta buga gasar zakarun Turai ba – a filin ne za ta fafata da Manchester City. Sai kuma filin was ana Bank of America Stadium yana daga cikin filin da Chelsea za ta gwada ‘yan kwallon da za ta yi amfani da su a badi – a nan ne za a kece raini tsakanin Chelsea da Real Madrid.