Kocin kasar Morocco, Walid Regragui ya bayyana cewa, kasar Afirka baki daya yake wakilta ba kasashen Larabawa kadai ba a gasar cin kofin Duniya da yanzu haka ake fafatawa a kasar Qatar.
Walid ya bayyana hakan ne yayin da manema labarai suka tambaye shi, ganin cewa Kasar da yake koyarwa ita daya ce tilo da ta rage a cikin kasashen bakar fata da Larabawa da suka samu nasarar shiga cikin gasar.
Walid ya shaida wa manema labarai cewa “Ba na zo nan don zama dan siyasa ba ne, muna so mu daga tutar Afirka ne kamar yadda Senegal, Ghana, Cameroon da mu (Morocco) muka zo nan. Muna nan don wakiltar Afirka baki daya.”
Kasar Morocco ta tsallaka zagaye mai kasashe takwas bayan lallasa kasar Spain da ci 3:0 a fanareti.