Jiya Talata 24 ga watan nan, ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya aike da sakon ta’aziyya ga ma’aikatar harkokin wajen kasar Gabon, bisa rasuwar ministan harkokin wajen kasar Michael Moussa-Adamo.
A cikin sakon ta’aziyyar, Qin Gang ya bayyana cewa, ya kadu matuka da samun labarin rasuwar minista Moussa-Adamo, ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa game da hakan, tare kuma da nuna juyayi ga ‘yan uwansa. Ya kara da cewa, minista Moussa muhimmin dan siyasa kuma jami’in diflomasiyya ne a kasar Gabon. Ya nuna matukar zumunci ga jama’ar kasar Sin, da sa kaimi ga zumuncin dake tsakanin Sin da Gabon, ya ba da muhimmiyar gudummawa ga bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ya ce kasar Sin na son yin hadin gwiwa tare da kasar Cabon, don inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, wajen kara samun sabbin sakamako. (Mai fassara: Bilkisu Xin)