• English
  • Business News
Wednesday, August 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Qin Gang Ya Halarci Taron Ministocin Wajen Kasashen Kungiyar SCO

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Qin Gang Ya Halarci Taron Ministocin Wajen Kasashen Kungiyar SCO
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Qin Gang, ya ce a halin da ake ciki, duniya na fuskantar tarin rigingimu da kalubale, kuma a matsayin ta na muhimmin jigo mai tasiri a harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi, ya zama wajibi kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, ta ingiza nasarar “Ruhin Shanghai “, ta gina al’umma mai makomar bai daya, musamman a gabar da harkokin kasa da kasa ke kara shiga yanayi mai sarkakiya da rashin tabbas.

A yau Juma’a ne dai Qin Gang ya yi wannan tsokaci, yayin da yake halartar taron ministocin wajen kasashe mambobin kugiyar ta SCO a birnin Goa na kasar India.

  • Xi Jinping Ya Jagoranci Zama Na Farko Na Kwamitin Koli Kan Harkokin Kudi Da Tattalin Arziki Karo Na 20

Qin Gang ya kuma jaddada cewa, Sin a shirye take, da ta ci gaba da fadada hadin gwiwa da sauran kasashe mambobin kungiyar, da kara aiki tare, kan turbar bunkasa kasa da kara. Kaza lika za ta ci gaba da aiki da sauran sassa, wajen ganin an cimma manufar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Yayin taron na wannan karo, mahalartansa sun yi duba na tsanaki kan gudummawar SCO, a matsayin ta na muhimmin dandalin shiyya dake ingiza tsaro da ci gaban yankin ta, sun kuma amince da bukatar kara karfafa hadin gwiwar tsaro, da ingiza hadin kai a sassan da suka hada da na sufuri, da makamashi, da hada hadar kudade, da zuba jari, da cinikayya maras shinge, da raya tattalin arziki ta fasahohin sadarwa.

Bugu da kari, dukkanin sassan sun goyi bayan Afghanistan, a burin ta na tabbatar da kwanciyar hankali da sake ginin kasa, yayin da suke mara baya ga SCO da ta karfafa hadin gwiwa da MDD, da kasashe mambobin kungiyar BRICS, wajen kare manufofi da ka’idojin MDD, da kuma martaba cudanyar dukkanin sassa. (Saminu Alhassan)

Labarai Masu Nasaba

Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Xi Jinping Ya Jagoranci Zama Na Farko Na Kwamitin Koli Kan Harkokin Kudi Da Tattalin Arziki Karo Na 20

Next Post

Sudan: Rukuni Na Biyu Na ‘Yan Nijeriya Sun Iso Abuja

Related

Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?
Daga Birnin Sin

Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

2 hours ago
Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

3 hours ago
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha
Daga Birnin Sin

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

5 hours ago
Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

5 hours ago
Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya
Daga Birnin Sin

Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

7 hours ago
Sassou Nguesso: Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC
Daga Birnin Sin

Sassou Nguesso: Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC

8 hours ago
Next Post
Sudan: Rukuni Na Biyu Na ‘Yan Nijeriya Sun Iso Abuja

Sudan: Rukuni Na Biyu Na 'Yan Nijeriya Sun Iso Abuja

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

August 26, 2025
Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

August 26, 2025
Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025

Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025

August 26, 2025
Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

August 26, 2025
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna

August 26, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

August 26, 2025
Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

August 26, 2025
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 26, 2025
Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

August 26, 2025
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

August 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.