A yau ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Qin Gang ya yi nuni da cewa, tun farkon wannan shekara, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ta fuskanci sabbin matsaloli da kalubale, kuma a bayyane yake wane ne ke da alhakin wannan lamarin. A ko da yaushe kasar Sin na nacewa ga ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya, da hadin gwiwar samun nasara da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, yayin duba da kuma tafiyar da dangantakar Sin da Amurka.
Qin Gang ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun Taiwan da sauran muhimman batutuwa dake shafar muradun kasar Sin, yana mai jaddada cewa, kamata ya yi Amurka ta mutunta ta, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da daina cutar da muradun kasar Sin ta fuskar tsaro da ci gaba da sunan takara. Kasar Sin na fatan bangaren Amurka zai dauki matakai na zahiri don aiwatar da muhimmin ra’ayi da alkawuran da shugabannin kasashen biyu suka dauka a taron Bali, da yin aiki tare da kasar Sin a kokarin yin hadin gwiwa.
Sannan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, zai kawo ziyara kasar Sin, tsakanin ranaikun 18 zuwa 19 ga watan Yunin nan, kamar dai yadda gwamnatocin Sin da Amurka suka amince da hakan. (Masu Fassarawa: Ibrahim Yaya, Saminu Alhassan)