Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sake kaddamar da kashi na biyu da dakarun tsaron Katsina Community Watch Corps guda 500.
Samar da ƙarin jami’an tsaron na da nufin ƙara inganta harkokin tsaro a wasu yankuna.
- Gwamnatin Tarayya Da EU Sun Kulla Yarjejeniyar Bunkasa Wutar Lantarki
- Yanayin Cin Abinci Da Baccin Annabi Muhammadu (SAW)
Da yake jawabi a wajen kaddamar da dakarun tsaron, Raɗda ya ce an samar da motoci guda 10 da kuma babura da bindigogi domin a kara tunkarar matsalar tsaro gadan-gadan.
A cewarsa, wannan tsarin da aka bullo da shi na samar da dakarun tsaron na C-Watch abu ne da suka yi tunanin idan aka haɗa hannu da sauran jami’an tsaro zai taimaka wajen matsalar tsaron da ake fama da ita.
“Alal hakika wadannan dakaru suna buƙatar addu’a da goyon baya domin su samu nasarar da ake buƙata ta magance matsalolin tsaro wanda suka yi wa tattalin arziki da harkar noma kamshin mutuwa a Arewacin Nijeriya.”
A jawabinsa, Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Hon. Nasiru Mu’azu Danmusa ya bayyana cewa an sake ɗaukar mutane 550 da suka fito daga ƙananan hukumomi 10 na jihar Katsina.
Kananan hukumomin sun haɗa da; Charanchi da Dutsinma da Kurfi da Musawa da Matazu da Malumfashi da Kafur da Bakori da Danja da kuma Funtua.
Ya ce matasan an yi tunanin samar da su domin tunkarar matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu yankuna na jihar Katsina.
Haka kuma Kwamishinan ya ƙara da cewa samar da dakarun tsaron na C-Watch na daga cikin alƙawarin da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓe inda ya ce tsaro na daga cikin abu mai muhimmanci.