A kwanan nan ne gwamnatin Tinubu ta bullo da batun yi wa haraji garambawul, lamarin da ya yi matukar ya ta da kura a kasar, inda gwamnatin ke faman shan suka a kowane bangare.
Meye ra’ayinku dangane da wannan lamarin Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne akan yadda gwamnatin Tinubu ta bullo da gyara kan lamarin haraji.
Usman Amar
Gyaran haraji yana da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasa idan an aiwatar da shi yadda ya kamata, kuma adalci ya tabbata akan hakan. Sai dai yadda mutane ke mayar da martani akan gyaran ya danganta da yadda aka bayyana manufar da kuma ko tana magance matsalolin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta, don gyaran haraji na gwamnatin Tinubu ya samu karbuwa, wajibi ne a tabbatar da gaskiya da adalci wajen raba nauyin harajin. Ya kamata a tabbatar cewa wannan tsari ba zai fi shafar masu karamin karfi ba.
Abdullahi Muhammad
Gyara a kan haraji da gwamnatin Tinubu za ta yi to ya danganta saboda a yanzu su kansu mutanen da za’a karbi harajin a wajensa abin da ake basu ba ya isarsu, ba ma maganar isa ake ba, ana magana sai dai a ce babu saboda kudin da zai sai maka abu goma alal misali yanzu bai fi ya sai maka abu biyu zuwa uku ba kuma ba kara maka kudi aka yi ba wannan dai wanda kake karba tuntuni shi ne dai to ta yaya ake so mutane su yi da ransu.
Sannan maganar haraji za za’a ce a yi gyara akan ba fa masu kudin abu zai karewa ba akan talakan abin zai kare, to ba fa maganar abubuwan rayuwa ake ba ana magana ne akan abin da za’a ci wato abinci, a yanzu haka akwai gidajen da sau daya suke cin abinci wani sau biyu masu dan hali kenan, akwai inda abincin ma babu kwata-kwata, sai dai abin da Allah ya bayar, to da wannan halin da muke ciki za’a fara maganar gyaran haraji, Allah ya sa mu dace amma a duba wannan lamari.
Abdurrahman Tijjani
Maganar gyaran haraji da gwamnatin Tinubu take neman kirkiro shi wannan magana gaskiya idan aka duba to talaka sai ya fi shan wahala saboda yanzu ma abin da yake samu ba ya isarsa ballantana kuma a ce za’a kara rage shi to sai abin da hali ya yi.
Mu dai don Allah muna roko da babbar murya akan ‘yan majalisa da su daure su ci gaba da jajircewa su yi kokari su saya akan bakansu kada su yadda da wannan al’amarin. Sannan ita kuma gwamnati ta duba wannan lamarin komai ta zartar kuma ya zauna, to wannan ta yi hakuri ta janye kudirinta da ta tausayawa lakawanta.
Rabi’atu Abdullahi
Maganar gyaran haraji, to ni dai a ganina kamar bai kamata a yanzu a ce za’a dakko wannan maganar ba saboda su kansu mutane albashin nasu ba ya kai musu ko’ina, a halin da ake ciki maganar karawa ma’aikata albashi ya kamata a yi ba wai rage musu ba, sannan shi kansa albashin ba maganar kara shi za’a yi ba sai dai a ce maganar saka albashi saboda wanda muke karba shi ne kari wanda za’a sa shi zai zama albashin saboda an shiga wata irin rayuwa ana cikin wani hali abin da da ka fi karfinsa amma a yanzu yafi karfinka, kuma da da na ce ba wai da can ba kwana-kwanan nan duka-duka shekara daya ce da ta wuce za’a, a lokacin misali idan abu Naira 100 yake to yanzu ya kusa nika kudinsa sau hudu ko biyar, to kin gani da me mutum zai ji kuma ganar nan da nake komai da kika sani na rayuwa haka ya zama sai dai addu’a, kullum idan ka shiga kasuwa sai ka tarar abu ya tashi a Nijeriyar nan haka muke fama.
To talaka ya zai yi da ransa sannan kuma yanzu a ce za’a bullo da wata maganar wai gyaran haraji mu dai don Allah gwamnati da makarrabanta ta duba wannan lamari sannan ya kamata su san halin da ‘yan Nijeriya suke ciki ba wai a yi ta yadda aka ga dama ba su dan suna cikin yalwa, to yakamata a duba na kasa.
Bilkisu Maharazu
Gyaran haraji yana da muhimmanci, ta wani bangaren kuma baya da shi idan muka yi la’akari da da can akwaishi ana an sa ba ana ba da shi aka zo aka rusa shi sai yanzu daga baya a ce ana so a farfado da shi, to da can shekarun baya me ya sa aka daina bayar da shi musamman na matafiya inda lokacin idan ban man taba kamar lokacin mulkin Obasanjo ne aka bukaci duk wani toll gate da ake amsar 10 ko 20 duk aka sa aka farfasa shi aka daina karbar komai wanda a lokacin mutane sun yi ta korafe-korafe akan hakan wanda har kafofin yadda labarai da na talabijin an nuna hakan saboda rashin jin dadin al,umma a wancan lokacin to kuma sai yanzu ace ana so adawo da shi saboda an raina wa mutane hankali don dai shi dan Nijeriya ba’a dauke shi a bakin komai ba. A gaskiya wannan lamarin akwai abin dubawa, sannan ba kowa zai yadda da haka ba.