Shawarar “ziri daya da hanya daya” ta jawo jarin kusan dala tiriliyan 1, da fitar da mutane miliyan 40 daga cikin kangin talauci. Kana kuma yayin yaduwar cutar COVID-19 a duk fadin duniya, kasashe da dama sun maida alluran riga-kafin kasar Sin da kayayyakin aikin jinyarta a matsayin abubuwan kare rayuwa. Duk wadannan al’amuran sun shaida cewa, ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya da kasar Sin ta hassasa, yana taka muhimmiyar rawa.
Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen kwalejin nazarin dangantakar kasa da kasa ta Moscow dake kasar Rasha a watan Maris din shekara ta 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya karo na farko, wanda ke kara samun habaka da bunkasa daga bisani, wato har sau shida aka rubuta shi cikin kudurorin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, kana, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba aka rubuta shi cikin kudurori ko sanarwa da aka fitar a wasu kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kungiyar hadin-kai ta Shanghai, da tsarin BRICS da sauran su, al’amarin ya samu amincewa da goyon-baya sosai daga gamayyar kasa da kasa. Ina dalilin da ya sa hakan ya faru? Takardar bayanin da gwamnatin kasar Sin ta bullo da ita a yau Talata 26 ga wata, mai taken “Gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya cikin hadin-gwiwa: Shawarar kasar Sin gami da matakanta”, ta bayyana muhimman ra’ayoyi da nasarorin da aka cimma wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, al’amarin da ya bada amsa ga wannan tambaya.
Ana bukatar sabon ra’ayi a sabon zamanin da muke ciki yanzu. Jirgi daya ya kwaso gaba dayan mu lokacin da muke fuskantar kalubale iri daya a duniya. Duk wahalhalu ko jin dadi, mu zama tsintsiya madaurinki daya da neman cimma moriya tare, ita ce mafita kadai. (Murtala Zhang)