A gobe Lahadi 31 ga watan Agustan nan ne kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, za ta gudanar da babban taro mafi girma tun kafuwarta. A matsayinta na kungiyar hadin gwiwa ta shiyya mafi yawan jama’a da fadin yankuna, SCO na gaggauta kara zama muhimmin jigo na inganta jagorancin duniya, inda take amfani da fifikon goyon baya, da hadin gwiwa a matsayin muhimman ginshikan shawo kan tarin kalubalen hadurra da matsaloli.
A matsayinta na wadda ta kafa kungiyar, har kullum kasar Sin na ci gaba da samar da gudummawar jagoranci, da ingiza ci gabanta. Sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a ya tabbatar da hakan, inda kaso 91.4 bida dari na masu bayyana ra’ayoyi daga kasashe membobin SCOn suka amince da gudummawar da Sin ke bayarwa, wajen cimma nasarorin dandalin, ta fuskar yayata matakai na zahiri na bunkasa hadin gwiwar membobinta, musamman ta fuskar kare tsaron yankinsu, da ingiza ci gaban tattalin arziki.
Tun kafuwar SCO, kungiyar ta wanzar da “Ruhin Shanghai” na mutunta juna, da cimma moriyar bai daya, da samar da daidaito, da tuntubar juna, da martaba mabambantan wayewar kai, da neman damar ci gaban bai daya.
Ra’ayoyin jama’a daga kuri’ar da kafar CGTN ta gabatar, sun shaida yadda kaso 86.8 bisa dari na masu bayyana mahangarsu suka amince da cewa, ‘Ruhin Shanghai’ ya samar da sabon salo, mara amfani da danniya da fito-na-fito, wajen aiwatar da jagorancin yanki a wannan duniya mai mabanbantan sassa masu tasiri. A daya bangaren kuma, kaso 81.8 bisa dari na ganin ‘Ruhin Shanghai’ na karfafa muryar kasashe masu tasowa, da samar da gudummawar gudanar da tsarin duniya madaidaici kuma mai adalci
Binciken jin ra’ayin jama’ar wanda kafar CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani, ya tattaro ra’ayoyin mutane 8,873 daga kasashen duniya 38. Ya kuma hado da ra’ayoyin al’ummun manyan kasashen duniya masu ci gaba, da ma na kasashe masu tasowa. Dukkanin masu bayyana ra’ayoyin na tsakanin shekarun haihuwa 18 ne zuwa sama, an kuma lura da yanayin kason kidayar al’ummun kasashen da kuma jinsinsu wajen tattaro ra’ayoyin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp