Bayan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a Jihar Kano ta bakin Ferfesa Ahmad Ibrahim Diko, babban jami’in tattara sakamakon zabe, inda bayyana cewa dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida) ya samu nasarar zama gwamnan Kano.
Abba Gida-gida ya samu kuri’u 1,196,002 wanda ta ba shi damar zama na daya a cikin sauran ‘yan takarar na jam’iyyu 18 da suka shiga takarar a Kano.
- Zaben Gwamna: PDP Za Ta Yi Zanga-Zangar Kwana 7 Kan Sakamakon Zaben Nasarawa
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
Sai kuma dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya zo na biyu da yawan kori’u 89,705, inda Sheikh Ibrahim Khalil ya na uku da yawan kuri’u da suka kai 10,836.
Sanarwar ta hukumar INEC ke da wuya sai wasu daga cikin ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban a Kano suka bayana ra’ayoyinnsu kan wannan nasarar Abba Gida-gida.
Daga cikin jam’iyyun da suka bayana ra’ayoyinsu kan zaben sun hada da jam’iyyar ADP wacce Sha’aban Sharada da ya zo na hudu, ya ce ya karbi kaddara kan wannan zabe.
Shi ma dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC, Shiek Ibrahim Khalil ce wa yayi haka Allah ya so, domin haka a shir yake ya ba da manufofinsa wajen ciyar da Kano gaba muddin an nemi haka a gareshi.
A yayin da Hon Muhammad sadik Wali, dan takarar gwamnan Kano na PDP, ya ce jam’iyyarsa ta yi kokarinta a zaben amma ba ta samu nasara ba. Ya ce birinsu a samu ci gaban Kano.
Jam’iyyar APC ta bakin, Barista Abdul ya bukaci INEC ta suke zaban na ranar Asabar, wand APC rashen Jihar Kano ta bayyana a matsayin wanda bai kammala ba.