‘Yan Nijeriya da dama sun yaba wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan matakin da ya dauka na rage yawan ’yan rakiyarsa a tafiye-tafiyensa na cikin gida da na kasashen waje, sai dai wasu suna tababa da wannan yunkuri na shugaban kasa domin kuwa an sha jin sanarwa masu kama da wannan amma ba a iya aiwatar da su.
Idan za a iya tunawa, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar zaftare kashi 60 cikin 100 na adadin mukarraban da za su rika yi masa rakiya na tafiye-tafiye da kuma mataimakinsa da sauran jami’an gwamnati.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da shugaban kasar ya sanar da rage yawan jami’an da za su rika yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je a ciki da wajen kasar.
- Tinubu Ya Bada Umarnin Binciken Ma’aikatar Jin Kai Kan Zargin Karkatar Da Miliyan N585
- Tinubu Ya Yi Alkawarin Garambawul A Bangaren Lantarki
Matakin ya kuma shafi dukkan ministoci da manyan jami’an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban kasa da uwargidan shugaban kasa, wadanda su ma ya ba da umarnin rage adadin jami’an da za su rika yi musu rakiya, kamar yadda Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban Nijeriya kan harkar yada labarai ya fitar a cikin wata sanarwa.
A cewar Ngelale, matakin wani yunkuri ne na rage yawan kudaden da jami’an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.
Sanarwar ta ce yawan jami’an da za su rika yi wa shugaban kasar rakiya zuwa kasashen waje, nan gaba ba za su wuce jami’ai 20 ba, yayin da ’yan rakiyarsa a tafiyar cikin gida ba za su wuce jami’ai 25 ba. Sannan kuma sanarwar na cewa Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a daina tura dimbin jami’an tsaro zuwa wata jiha a duk lokacin da zai kai ziyara can, maimakon haka za a rika amfani da jami’an tsaron da ke jihar ne kawai don tabbatar da tsaro.
Wannan mataki na zuwa ne makonni biyar bayan da ‘yan Nijeriya suka soki gwamnatin Tinubu na daukan wakilai 1,114 zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya a Dubai, duk da yake fadar shugaban kasa ta ce wakilai 422 kawai ta dauka, rahoton dai ya ce an kashe naira bilyan 2.78 a kudin jirgi.
Wasu ‘yan Nijeriya sun bayyana ra’ayoyinsu mabambanta kan wannan lamari.
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun zuba ido su gani ko za a yi aiki da matakin kar ya zama na fatar baki kawai.
Ya ba da shawarar a kafa wani sashe na musamman a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda zai rika sa ido tare da tabbatar da cewa sauran shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun yi aiki da sabon matakin na shugaban kasa.
Abubakar Sabo ya ce, “Wannan abun a yaba ne, amma sai an aiwatar sannan nan zan nuna godiyata”
Tukur Abdu Zaria, cewa ya yi “Mu gani a kasa wai ana biki a gidan su kare”
Rukayya Shehu ta ce “Da za a aiwatar da wannan kuduri da mun ji dadi”Bashir Dalhatu ya ce “Allah dai ya sa a yi amfani da kudaden wajen inganta ilimi da samar da tsaro da samar da ayyukan yi ga matasa don kuwa shi ne babban matsalar kasar nan”.