A cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin ta samu ci gaba sosai a fannin kiwon lafiyar mata da kananan yara. Inda yawan mace-macen mata masu juna biyu ya ragu da kusan kashi 4 cikin dari a ma’aunin shekara-shekara, kana shi ma adadin mace-macen jarirai da yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu da kusan kashi 5 cikin dari.
Mahukuntan lafiya na kasar sun bayyana cewa, a shekarar 2024, kasar Sin ta yi kokarin rage mace-macen mata da ake samu lokacin haihuwa zuwa kashi 14.3, watau wadanda aka samu daga cikin haihuwa 100,000 ba su wuce guda 14.3 ba. Haka nan a bangaren yara ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa, an samu raguwar mutuwarsu da ta kai kashi 5.6 cikin dari a tsakanin yara 1,000.
- Ba ‘Yan Nijeriya Ne Ke Kai Mana Hare-hare A Benuwai Ba – Gwamna Alia
- 2024: Manyan Alkaluman Sufuri 2 Na Filayen Jiragen Sama Na Kasar Sin Sun Kafa Tarihi
Abin da ya kamata a sani shi ne, ba da rana tsaka kawai kasar Sin ta samu wadannan nasarori ba, ta yi tsari da aiwatar da shirye-shirye masu kyau wajen kula da lafiyar mata da yara na kasar. Bisa kididdigar da hukumar lafiya ta kasar Sin fitar, a halin yanzu kasar Sin tana da cibiyoyin kula da mata masu fama da matsananciyar cuta guda 3,491, da cibiyoyin jinyar jarirai masu fama da rashin lafiya mai tsanani 3,221.
Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci.
Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin likitocin sun taimaka wajen haihuwar jarirai 63,800.
Tabbas, tsarin kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara na kasar Sin ya ba da kyakkyawan misali ga kasashen da ke neman inganta kiwon lafiyar mata da yaran, musamman ma ta fuskar tabbatar da cewa iyaye mata suna samun cikakkiyar kulawa lokacin goyon ciki da karbar haihuwa kyauta, da mayar da hankali a kan rigakafi, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu sosai.
Kazalika, bayan ayyukan kiwon lafiya, har ila yau tsare-tsaren kasar Sin na kawar da talauci a tsakanin al’ummarta suna ba da gudummawa ga inganta kiwon lafiyar mata da yara. Ta hanyar cike gibin tattalin arziki a tsakanin jama’arta, iyaye mata masu karamin karfi suna samun kulawar da ta dace ba tare da fargabar matsalar kudi ba. Tsarin kasar Sin dai ya gabatar da darussa masu kima ga kasashen da ke son bin sawu musamman ma masu tasowa da kuma masu rauni. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp