Sanin kowa ne cewa Nijeriya na cikin tarnaƙin fatara da yunwa. Ba kowa ba ne ya ke iya ciyar da kan sa da iyalin sa, ballantana ya gudanar da wasu harkokin na rayuwa. Akwai ma masu cewa Nijeriya ta fi kowace ƙasa fama da fatara a duniya. Duk da yake hakan ba gaskiya ba ne, amma yanayin da ake ciki ya sanya tilas shugabanni su fito da hanyoyin rage halin ƙunci da ake fama da shi.
- APC Ta Gamsu Da Bayanan Da Tinubu Ya Bayar A Gaban Kwamatin Tantance ‘Yan Takara
- Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Shugabancin Jam’iyyar APC Ta Kasa
A daidai lokacin da gwamnatin Buhari ta zo, duniya gaba ɗaya ta auka cikin halin karayar tattalin arziki saboda faɗuwar farashin man fetur. A cikin 2016 ƙasar ta faɗa cikin ramin karayar tattalin arziki wanda ba ta taɓa ganin irin sa ba a tsawon shekaru 25. Masana sun ce tattalin arzikin mu ya tsuke da kashi 1.6 cikin ɗari inda kashi 43 cikin ɗari na jama’ar ƙasar (wanda ya kama mutum miliyan 89) su ke rayuwa cikin matsanancin talauci, sannan wasu kashi 25 cikin ɗari (mutum miliyan 53) su ke gab da faɗawa cikin irin wannan mugun yanayin.
Ko a wannan shekarar ta 2022, Bankin Duniya ya fitar da wani rahoto inda ya ce yawan ‘yan Nijeriya masu fama da fatara zai ƙaru zuwa mutum miliyan 95.1 a bana kaɗai. A rahoton, mai taken ‘Don Inganta Rayuwar Dukkan ‘Yan Nijeriya: Nazari kan Fatara a Nijeriya a Cikin 2022’ (a turance, ‘A Better Future for All Nigerians: 2022 Nigeria Poverty Assessment’), rahoton ya nuna yadda faruwar annobar korona (COVID-19) ya ƙara ta’azzara yanayin fatara da yunwa a Nijeriya, ta yadda an samu qarin mutane miliyan 5 da su ka auka cikin ƙangin fatara.
Rahoton ya ce saboda karyewar tattalin arzikin ƙasashen duniya baki ɗaya, ko da a ce annobar korona ɗin ba ta zo ba, za a samu ƙarin matalauta daga mutum miliyan 82.9 a shekarar 2018/19 zuwa miliyan 85.2 a shekarar 2020 da miliyan 90 a cikin 2022, musamman saboda ƙaruwar yawan jama’a da ake samu. To amma kuma saboda faruwar annobar sai ya kasance fatara ta ƙaru daga kashi 40.1 cikin ɗari a cikin 2018/19 zuwa kashi 42.0 cikin ɗari a 2020 da kuma kashi 42.6 cikin ɗari a 2022, wanda hakan ya nuna cewa matalauta miliyan 89.0 ake da su a cikin 2020 kuma za su ƙaru zuwa miliyan 95.1 a cikin 2022. Don haka, annobar ita kaɗai ta tura ƙarin ‘yan Nijeriya miliyan 3.8 cikin fatara a cikin 2020, da ƙarin mutum miliyan 5.1 da ke cikin fatara a cikin 2022.
Bankin Duniya, wanda ya ƙunshi masana harkar tattalin arziki, ya bada shawarar cewa lallai ne gwamnati ta fito da hanyoyin rage matsin fatara da ke damun mutane masu ƙaramin ƙarfi. An shawarce ta da ta fito da wasu tsare-tsare da za su taimaki talaka, musamman wajen samar da aikin yi da taimaka wa manoma da ma ayyukan gida da ba su shafi noma ba, da samar da kayan more rayuwa irin su wutar lantarki da hanyoyin sufuri.
Bankin ya ƙara da cewa lallai ne gwamnati ta samar da yarda da aminci a tsakanin ta da waɗanda ta ke yi wa mulki, kuma ta aiwatar da shirye-shirye waɗanda mutane za su gani a ƙas har su yarda da su.
A bisa irin waɗannan shawarwari, tun a cikin 2016 gwamnatin Buhari ta fito da Shirye-Shiryen Inganta Rayuwa na Ƙasa, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIP), wanda wani gungun tsare-tsare ne da aka ƙirƙira don nemo tushen fatara da ke tofo a ƙasar nan a sare shi. Waɗannan muhimman shirye-shirye an ɗora alhakin aiwatar da su ne a wuyan sabuwar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya.
Tsare-tsaren wannan shiri na NSIP su na da yawa (irin su N-Power da bada tallafi ga matan karkara). Ɗaya daga cikin su shi ne Shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta, wato a turance ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHSFG). A ƙarƙashin wannan tsarin, an riƙa ciyar da ɗaliban makarantun firamare na gwamnati ‘yan aji 1 zuwa aji 3 a kullum, wato daga Litinin zuwa Juma’a. A kan kashe N70 wajen bai wa yaro abincin rana.
Abin mamaki shi ne, duk da irin alfanun da ke tattare da shirin (wanda za mu yi maganar su nan gaba kaɗan), sai ya kasance wasu ‘yan Nijeriya su na sukar sa, su na cewa ba su ga amfanin sa ba. Na ga suka kala-kala musamman a makon jiya lokacin da ma’aikatar ta bayyana ƙarin kuxin abincin kowane yaro daga N70 zuwa N100. Kanun labaran da jaridu su ka buga, wato za a kashe naira miliyan 999 wajen ciyar da ‘yan makaranta a kowace rana, ya ɗauke hankalin jama’a, har wasu na cewa, “Kawai an fito da sabuwar hanyar sata!” Wasu kuma sun ce maimakon wannan shirin ciyarwar, a karkatar da kuɗin zuwa ga wani shirin na daban.
Da yawa masu sukar shirin sun kalli yawan kuɗin da aka ce za a riƙa kashewa ne, ba tare da la’akari da yawan ɗaliban da za a ciyar ba, wato yaro miliyan 10 a kowace rana. Haka kuma da yawa ba su fahimci shirin ba ballantana su gane alfanun sa. Wasu kuma tsantsar adawa ce kaɗai ke cin su.
Kamar yadda na faɗa, wannan shiri wani ɓangare ne na babban shirin rage raɗaɗin fatara a Nijeriya, wato ba shi kaɗai ba ne, domin akwai wasu waɗanda Ma’aikatar Jinƙai ke aiwatarwa. Dukkan waɗannan tsare-tsare su na cimma nasara, kuma ba za ka gane hakan sosai ba har sai ka tattauna da wanda ya ke cin moriyar su.
Babbar manufar fito da shirin ciyar da ‘yan makarantar firamare ‘yan aji 1 zuwa 3 shi ne a qarfafa wa iyaye matalauta su riƙa barin ‘ya’yan su su je makaranta. Iyaye da dama ba su iya ɗaukar nauyin kai ‘ya’yan su makaranta, musamman idan ba su iya ba su kuɗin abinci da ake kira “kuxin tara” wanda yara ke ci a makaranta. Ɗauke masu wannan nauyin ba ƙaramin sauƙi ba ne a gare su.
Su kan su yaran, wani yaron ko don ya samu wannan abincin mai daɗi zai iya sanya shi ya riqa ɗokin zuwa makarantar, ya zauna a ciki har ya yi karatun. Yanzu ma da aka ce za a riqa bada ƙwai ga kowane yaro a duk ranar Laraba, abincin nasu ya ƙara armashi.
Idan kai ka fi ƙarfin irin wannan abincin, kila ba za ka fahimta ba. Amma ka tambayi waɗanda abin ya shafa, ka ji yadda su ke ji a ran su.
A bara, gwamnatin Jihar Kano ta bayyana irin alfanun da ke tattare da shirin ciyar da ɗaliban. Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Muhammad Salisu Ƙiru, ya ce shirin ya haifar da ƙaruwar shigar da yara makarantar firamare ‘yan aji 1 zuwa 3 daga yara miliyan 1.2 zuwa miliyan 2.9. Ya ce musamman ya kafa wani kwamiti wanda ya tabbatar da wannan ƙarin da aka samu. Ya ce, “Na san yara na da tunani sosai idan sun ji ana bada abinci kyauta za su so su riƙa zuwa makaranta domin koyon karatu.” Ya ƙara da cewa gwamnatin Jihar Kano na karɓar naira biliyan 1.5 a duk wata daga hannun Gwamnatin Tarayya.
A da fa kenan, lokacin da N70 ake kashewa wajen ciyar da kowane yaro. Yanzu saboda tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci, aka ga tilas ne a ƙara kuɗin da N30, wato ya koma N100. Shin ko a hakan ma, ina ne za ka je ka ci abincin N100 ka qoshi? Masu cewa ana kashe kuɗi ba kan-gado sun manta da hauhawar farashin da kayan abinci ke yi ne. Ko waye aka ce ya ciyar da yaro da N100, har ya ɗan samu riba a matsayin sa na ɗan kwangila, zai yi kukan cewa kuɗin sun yi kaɗan. Ga shi kuma Bankin Duniya ya ce fatara za ta ƙaru a bana; gobara daga kogi kenan, maganin ta Allah!
Sannan masu cewa kashe naira miliyan 999 a rana ɗaya kuɗin ya yi yawa, ba su yi la’akari da yawan ɗaliban ba ne. Ɗaliban firamare a duk faɗin Nijeriya fa aka ce, kuma ɗalibai miliyan goma. To kai mai suka idan kai ne, nawa za ka kashe?
Wani abu da mutane ba su gane ba shi ne ba fa Ministar Harkokin Jinƙai, Sadiya Umar Farouq, ba ce za ta kashe kuɗin ko kuma ma’aikatar ta ce za ta riƙa kashe kuɗin. Rashin sanin haka ya sa wasu na zargin cewa wai ministar za ta wawure kuɗin ne kawai.
Amma a yadda ake gudanar da tsarin, ita Ma’aikatar Jinƙai aikin ta shi ne ta rarraba kuɗin ga gwamnatocin jihohi, su ne su ke aiwatar da aikin ciyarwar, domin fa ɗaliban firamaren duk nasu ne, ba na Gwamnatin Tarayya ba; su ne su ka san ɗaliban nasu da inda su ke.
Kuma ko su gwamnatocin jihohin, ba su ba ne za su kashe kuɗin kai-tsaye ta hanyar bada kwangilar dafa abinci da raba shi a makarantu. Akwai kwamiti a ko wace jiha da ya ɗunshi jami’an gwamnatin jihar da na tarayya, da kuma wakilan ƙungiyoyi masu zaman kan su da sauran su.
’Yan wannan kwamitin, su na zaune a jiha, su na jiran isowar kuɗin daga Gwamnatin Tarayya. Da ma sun gama shirin su tsaf: sun tantance ɗaliban da makarantun da ‘yan kwangilar. Don haka da zaran kuɗi ya zo, sai aiki kawai. Saboda haka, kamar yadda babu ruwan minista da wannan kuɗi, to shi ma gwamna ba ruwan sa. Haka kuma babu ruwan wani kwamishina ko hedimastan firamare da wannan kuɗi. Kuɗi ne da ba su ciwuwa irin yadda wasu mutane su ke tunani.
Wani babban alfanun wannan shirin shi ne yadda ya yi naso a cikin tsarin tattalin arzikin ƙasa. A nan, ina nufin yadda mutane iri daban-daban za su amfana da shirin ta fuskar aikin da su ke yi wa shirin. Na farko, an ɗauki ma’aikatan shirin, an rage masu zaman kashe wando; na biyu, an ɗauki mata masu girka abinci aiki. Ga ‘yan kwangila masu sawo kayan abincin. Manoma ma za su amfana domin za a riƙa sayen kayan da su ka noma a cikin daraja, ana kaiwa makarantu domin girkawa.
Ka ɗauki masu kiwon kaji, a ƙaramin misali. A kowace Laraba, za a raba ƙwai guda miliyan 10 ga ɗalibai duk a faɗin Nijeriya. Don tabbatar da ingancin ƙwan da kuma tsare gaskiya wajen sayen sa, za a riƙa sayen ƙwan ne ta hanyar ‘ya’yan Ƙungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya (Poultry Association of Nigeria).
Waɗannan ƙwai miliyan 10 da za a saya a duk mako ɗaya, ba ƙaramar taimaka wa makiyayan kaji zai yi ba; lallai aljifan su za su yi nauyi!
Ko ta ina dai idan ka kalli wannan tsarin, za ka ga cewa nagge daɗi goma ne, domin ya na wanzar da alfanu ba guda ɗaya kacal ba. Zai taimaka wajen rage raɗaɗon fatara, ba ga iyaye da ɗalibai kaɗai ba, har ma ga manoma da masu dafa abinci da mahauta da ‘yan kwangila da masu jigila da mota da sauran su. Ƙarfafa hanyoyin tattalin arzikin jama’a ya na daga cikin manufofin tsarin. Ganin tasirin sa a rayuwar jama’a ne ma ya sa Bankin Duniya ya yaba da shi, ya ke tallafa masa da shawarwari da kayan aiki da kuɗi. Idan har mutum ya kafe a kan cewa bai ga amfanin shirin ba, to ko dai adawa ke damun sa ko kuma bai ilmantu kan manufar shirin ba.
A sabon garambawul ɗin da aka yi wa shirin kwanan nan ke aka ƙudiri aniyar ƙara kuɗin ciyar da ɗalibi daga N70 zuwa N100. Kuma ba Ma’aikatar Harkokin Jinƙai kaɗai ce ta zauna ta yanke hukuncin hakan ba, sai da ta zauna da wakilan masu ruwa da tsaki a tsarin, wato irin su da Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (World Food Programme), da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (National Bureau of Statistics), da Hukumar Faɗakarwa ta Ƙasa (National Orientation Agency, NOA), da Ƙungiyar Inganta Abinci ta Duniya (Global Alliance for Improved Nutrition, GAIN), da Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, da ma wasu. Saboda haka, wannan shiri ne wanda kowa ya dace ya yi na’am da shi don ɗimbin alfanun sa ga jama’ar Nijeriya.
·Ibrahim Sheme ɗan jarida ne mazaunin Abuja