Duk da raguwar hauhawar farashin kayayyaki da aka samu karo na hudu a jere a Nijeriya, ‘yan kasar da ‘yan kasuwa ba su samu saukin da ake tsammani yadda ya kamata ba.
Rahotanni sun nuna cewa hauhawar farashi ya ragu zuwa kaso 21.88 a cikin 100 a watan Yuli daga kaso 22.22 a watan Yuni.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Sanata Wadada Ya Fice Daga Jam’iyyar SDP Bayan Ganawa Da Tinubu
Tawagar Shugaban kasa Bola Tinubu sun nuna farin cikinsu da raguwar tare da misalta hakan bisa kyakkyawar tsarin shugabanci da kasar ke samu tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Wannan kuma na zuwa ne a yayin da tattalin arzikin kasar ya karu zuwa naira tiriliyan 372.8 a shekarar 2024 kuma ya sake samun tagomashi a watan Yulin 2025.
Kila wannan dalilin ne ya sanya tsohon ministan kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce, tattalin arzikin Nijeriya na daidaituwa, a lokacin da ta ziyarci Shugaban kasa Tinubu a kwanakin baya.
Duk da wannan matakin, ‘yan Nijeriya da ‘yan kasuwa na ci gaba da nuna damuwa kan cewa ba su ga alamar raguwar hauhawar a zahirance cikin tattalin arziki ba.
Farashin kayayyakin bukata daga na abinci zuwa na mai ba su yi sauka sosai yadda jama’a suke fata ko suke tsammani ba, hakazalika, kudin wuta, da tsadar kudaden sufuri duk suna nan ba sauki, sannan farashin makamashi dukka haka nan.
Da yake tofa albarkacin bakinsu, tsohon shugaban cibiyar hada-hadar banki a Nijeriya (CIBN), Mazi Okechukwu Unegbu da babban jami’in gudanarwar SD & D Capital Management, Gbolade Idakolo da fitaccen masanin tattalin arzikin nan, Farfesa Segun Ajibola, sun bayyana ra’ayoyinsu kan raguwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a watan Yuli.
A bangarensa, babban jami’in gudanarwar SD & D Capital Management, Gbolade Idakolo, ya bayyana cewar hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya na ci gaba da karuwa sakamakon matsalolin tsaro da kuma kalubalen farashin canjin kudade a yankunan da ake fitar da amfanin gona.
“Ainihin hauhawar farashin kayayyaki ya ragu a karo na hudu a jere ne saboda matsayin Babban Bankin Nijeriya kan MPR da sauran ayyukan da suka shafi tattalin arziki.
“Duk da haka, hauhawar farashin kayan abinci na ci gaba da hauhawa saboda rashin tsaro a yankunan noma da kuma kalubalen musayar kayan amfanin gona da ake shigo da su daga kasashen waje.
“Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta zage damtse wajen fito da shirye-shiryen da suka dace da zai kai ga rage tsadar kayan abinci a kasar nan,” ya shaida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp