Allah Ta’ala ya ce “duk wanda ya bi wannan Manzon, ya bi Allah ne”. Allah Ta’ala ya ce “ba mu aiko ka ba face kai rahama ne ga dukkan talikai.”
Malam Abubakar Shadibi ya ce “Allah ya kawata Annabi Muhammad (SAW) da ado na jinkai, sai shi kansa ya zamo Rahama, duk dabi’o’insa Rahama ne, siffarsa ma Rahama ce ga halitta, duk wanda wani Abu ya same shi daga wannan Rahama ta Annabi (SAW) ya tsira duniya da lahira daga dukkan abin ki. Duk wanda ya sadu da dabi’o’in nan na Manzon Allah abin so ne dukkansa. Shin ba ka gani ba Allah yana cewa “ba mu aiko ka ba face kai jinkai ne ga al’umma”. Sai rayuwar Manzon Allah (SAW) ta zamo Rahama, komawarsa ga Allah ma ta zamo Rahama Kamar yadda ya fada cewa “rayuwata alheri ce gare ku, rasuwata ma alheri ce gare ku”. Da kuma yadda Manzon Allah (SAW) ya ce “idan Allah ya so Rahama ga al’umma sai ya karbi ran Annabinta kafin al’ummar; sai ya sanya shi marigayi ko magabaci mai gyara gare ta (wanda zai shirya ma al’ummar komai a wurin Allah).
- Daga Cikin Mutane Aka Aiko Manzon Allah Amma Ba Mutum Ne Kamar Kowa Ba (SAW)
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 5 Kan Mallakar Bindigu Kirar AK-47 Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Allah ya yi wa Annabi ado da abubuwa da yawa amma babu kamar jinkai, shi ya sa ba don jinkansa ba (SAW), da duk wuta za a watsa mu. Domin duk abin da wata al’ummar da ta shige ta aikata aka halakar da ita, mu wannan al’ummar muna aikatawa har ma mun dara su. Amma jinkan Annabinmu (SAW) ne ya tserar da mu.
Shi ya sa idan aka yi laifi, sai a nemi wani uzuri a kai, kamar yadda uwa ba ta son ganin laifin danta kuru-kuru saboda jinkai, muma haka muke a wurin Annabi (SAW) har ma mun dara nan.
Shedan ya taba ce wa Ubangiji, “Ina mamakin Bayinka, suna son ka amma ba su bin umurninka, ni kuma suna ki na amma suna bin umurnina”, sai Allah ya bashi amsar cewa “Na yi rantsuwa da Zatina, na gafarta musu bin ka saboda kin ka da suke yi, ni kuma na yafe musu saboda so na da suke yi (Tabaraka wa ta’ala)”.
Wannan ba yana nufin mutane su kama yin sabo ba ne, a’a, lallai a kiyaye. Abin da ya sa ake fadar irin wannan saboda Manzon Allah (SAW) ya ce, “Fiyayyen mutane shi ne wanda zai soyar da mutane Allah kuma ya soyar da Allah mutane”, ma’ana wanda zai fada musu falalar Allah su so shi, idan sun so Allah kuma, Allah zai so su.
Duk wadannan Malaman da muke kawo bayanansu su ne Magabata Nakwarai, domin sun fi shekara dubu da rasuwa.
Malam Samarkandi ya ce ma’anar ayar da ta ce Manzon Allah rahama ne ga halitta, Allah yana nufin wannan halittar ba mutum ba kawai har da aljan. Watakila kuma aka ce ba su kadai ba kawai, ana nufin har da dukkan halitta baki daya, ma’ana duk wani abin da ba Allah ba, to Manzon Allah (SAW) rahama ne gare shi.
Manzon Allah rahama ne ga Mumini saboda ya shiryar da shi. Manzon Allah rahama ne ga Munafuki don ya samu amana saboda shi (SAW), kuma asirinsa ya rufu har zuwa lokacin da ya ko zai tuba wanda ba don haka ba da watakila an kashe shi. Manzon Allah rahama ne ga Kafiri saboda an jinkirta ma sa azaba. Kafiran zamaninsa (SAW) ‘yangata ne a kan Kafiran sauran Annabawa, ana ba su lafiya da arziki har ma Allah ya ce ba domin kar zuciyar Musulmi ta buga ba; da an hore ma Kafiran su rika zama a gidan zinare; abin kwanciyarsu ya zama zinare; haka nan abin hawansu. Allah zai yi haka ne ba don wata daraja ba gare su sai don ya nuna wa Musulmi cewa duniya ba komai ba ce. Duk wannan saboda rahamar Manzon Allah ce.
Abdullahi bin Abbas (RA) ya ce Manzon Allah rahama ne ga Muminai da Kafirai domin an baiwa kafiran zamaninsa lafiya ta yadda irin azabobin da aka yi wa kafiran baya da suka karyata Manzanni su ba a yi musu ba. Kamar kifar da su, mayar da ruwansu jini, kwarkwata ta cika gari ko kuma kwadi su cika duk abincinsu.
An ruwaito cewa Annabi (SAW) ya tambayi Mala’ika Jibrilu (AS) cewa “shin kai ma ka samu wani abu daga rahamar nan tawa?”, Jibrilu ya amsa da cewa “Na’am (Eh), tun da na ga abin da ya samu shugabanmu Iblis (kafin Allah ya kore shi) nake jin tsoron karshena, – amma – sai na amince (na san zan gama lafiya) saboda kirarin da Allah ya yi mun wanda albarkar zuwanka Alkur’ani ya sauka; a ciki Allah ya ce – ni Jibrilu – “Ma’abocin karfi ne wajen Ubangiji mai Al’arshi mai tabbatacciyar daraja. Abin bi ne; amintacce ne.”
Jibrilu ya ce daga rannan ya san cewa shi amintacce ne kuma ya aminta daga dukkanin abin tsoro.
Wannan yana kara jaddada rahamar Manzon Allah (SAW) ga dukkan halitta.
An ruwaito daga Ja’afar bin Muhammad Assadik (RA) cikin fadin Allah (SWT) a Suratul Waki’ah “fasalamul laka…” zuwa karshen ayar, ma’anarta ita ce “amincin ya zo wa mutanen bangaren dama (wadanda za su shiga Aljanna) ne saboda kai (Manzon Allah SAW). Ma’ana; kubutar Muminai ta tabbata ce saboda Manzon Allah. Ayyukanmu ba za su wadatar ba wurin aunawa har sai an samu ceton Annabi (SAW).
Sayyidina Ja’afarus Sadik yana bayani ne kan cewa duk wadanda za su samu rahama a ranar Alkiyama; za su samu ne saboda Annabi Muhammad (SAW). Wannan girmamawa ne gare shi (SAW).
Aya ta 35 cikin Suratun Nuur da take magana a kan “Allah ne hasken sama da kasa, misalin haskensa…”, Ka’abul Ahbari da Abdullahi bin Jubair (RA) sun ce “abin da ake nufi da haske na biyu da ya zo a cikin ayar shi ne Annabi Muhammad (SAW)”.
Sahalu bin Abdullahi Tustari ya ce ma’anar “Allah ne hasken sama da kasa” ita ce “Allah ne mai shiryar da mutanen sama da kasa”, fassarar “misalin haskensa” a cikin ayar kuma ana nufin Annabi Muhammad SAW (kamar yadda su Ka’abu da Abdullahi bin Jubair suka tafi a kai) yayin da yake ajiye a cikin tsatson mazaje da mahaifan mataye, ya zama kamar Alkuki ne (wato taga wadda ba ta huda bango ba da mutanen da suke amfani da shi wajen ajiye fitila ko a-ci-bal-bal) da fitila mai haske a cikinsa, wannan hasken yana nufin zuciyar Manzon Allah (SAW) (saboda zuciyarsa ta dau hasken sanin Allah da shari’ar Allah SWT). Zuciyar kamar fitila ce a cikin gilas, ma’anar gilas din ana nufin kirjin Manzon Allah (SAW), kirjin kuma kamar tauraro ne mai tashin haske saboda imani da Allah da ke ciki, da hikima (ma’arifa, wato ilimin sanin Allah. Wannan fitilar har ila yau ana kunnota ne daga bishiya mai albarka, ita bishiyar tana nufin Annabi Ibrahim, ma’ana an dosano hasken Manzon Allah ne daga hasken Annabi Ibrahim (dama shi (SAW) jikan Annabi Ibrahim ne). Dangane da fadin Allah cewa “man fitilar ya kusa ya yi haske shi kansa koda ba a kunna fitilar ba”, yana nufin Annabtar Manzon Allah (SAW) ta kusa ta bayyana ga mutane tun kafin ya bayyana musu sakon Manzanci”, kamar yadda Sahalu ya yi bayani.
Babu halittar da ta isa ta iya daukar irin imanin da ke cikin zuciyar Annabawa. Haka nan sauran mutane ba za su iya daukar imanin da ke zuciyar Siddikai da Waliyyai ba).
Ma’anar hasken nan da ke jujjuyawa a tsakanin mazaje da mataye, ana nufin duk wanda yake dauke da Manzon Allah (SAW) a tsatsonsa ko kuma idan mace ce ya shiga mahaifarta, sai bayanta ya kasance kamar Alkuki ne da aka ajiye fitila mai haske wadda za ka ga hasken nan yana hudowa waje ta baya.
A wurin wasu Malaman Tafsirin, ma’anar ayar “Allah ne hasken Sama da kasa…” tana nufin Allah ne mai haska sama da kasa.
Watakila kuma wasu malaman tafisirin sun yi tafsirin ayar daban da na Sahalu.
Alkur’ani ba a ma sa fassara da ra’ayi, ma’ana mai fassara ya rika cewa “a ganina”. Idan aka ba da damar hakan, masoyi zai fassara bisa yadda ya yi masa dadi a ransa, shi ma kuma makiyi sai ya yi fassarar ta yadda zai karkatar da ma’anar ayoyin da ke ciki. Shi ya sa dole a bi fassarar da manyan malamai suka yi; domin wasu ayoyin ma mutashabihatun ne, ba za su fassaru daidai da ma’anarsu ba in ba a wurin malamai ba wadanda su kuma suka ji daga Annabi (SAW).
Allah ya ambaci Manzon Allah (SAW) a matsayin haske, a matsayin fitila; ba a wannan ayar kadai ba. Haka yake, shi hasken ne (SAW) domin da yawa zai shiga wuri mai duhu sai a ga duk abin da yake wurin saboda haskensa. Sayyida Aisha (RA) ta ce “ina cikin dinki allurata ta fadi, na dauko fitila in duba sai ta mutu, sai ga Annabi (SAW) ya shigo, da hasken fuskarsa na ga allurar tawa.”
Malamai sun ce, hikimar abin da ya sa Allah ya kira shi da haske da fitila ita ce; yanzu idan aka kunna fitila guda daya, za a iya kunna milyoyin fitilu daga hasken wannan fitilar. Don haka duk wanda ka gan shi da haske, ya dosani haskensa ne daga hasken Annabi (SAW).
A cikin Suratul Ma’ida, karshen Aya ta 15, Allah (SWT) ya ce “hakika (wallahi) wani babban haske ya zo muku daga Allah tare da littafi mai bayyana muku dukkanin rayuwarku da shari’o’inku baki daya”.
Manzon Allah (SAW) da Alkur’ani duka sun zo ne daga Allah (SWT), Alkur’ani maganar Allah ne, shi kuma Manzon Allah (SAW) Ma’aikin Allah ne. A cikin ayar, Allah (SWT) ya ambaci Annabi (SAW) a matsayin haske.