Gwamnatin Tarayya ta nada jarumar Fina-finai, Rahama Sadau matsayin daya daga cikin shugabannin kwamitin bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar fasaha da basirar zamani.
Sadau ta samu wannan matsayi ne bayan wani zama da suka yi da mataimakin shugaban kasa, Sen. Kashim Shettima tare da sauran manyan mutane a fadar gwamnati inda aka tabbatar mata da matsayin tare da sauran ‘yan kwamitin.
- Sojoji Na Zargin Sarakuna Da Hannu A Kisan Dakaru 17 A Delta
- Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Mutane 12 Da Dukiyar Miliyan 130 A Kano
Da wannan ne jaruman Kannywood da suka samu matsayi a gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu suka zama biyu da suka hada da Ali Nuhu wanda ya samu shugabancin hukumar Fina-finai ta Nijeriya a watan Janairu.
An dorawa kwamitin mai suna Investment in Digital and Creative Enterprise hakkin zakulo yan Nijeriya masu fasaha musamman matasa domin habaka tattalin arzikin kasa ta hanyar fasaha da basirar zamani a wannan karni.