Gwamnatin jihar Kano ta amince da kafa kwamitin wayar da kan jama’a kan yin rajistar katin kaɗa ƙuri’a domin karfafa gwiwar ‘yan jihar baki daya wajen gudanar da rijistar katin zabe.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin majalisar zartarwar jihar, Musa Tanko ya fitar, kwamitin ya nada kwamishinan yada labarai, Abdullahi Waiya a matsayin shugaban kwamitin.
- Safarar Yara: Gwamnatin Adamawa Ta Haɗa Yara 14 Da Iyayensu Da Aka Ceto A Anambra
- Xizang A Shekaru 60 Da Kafuwa: Daga Mawuyacin Hali Zuwa Farin Wata Sha Kallo
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, sakataren gwamnatin jihar (SSG) ne zai kaddamar da kwamitin a hukumance a lokacin da ya dace kuma za a dora masa alhakin tabbatar da samun nasara da kuma tabbatar da cewa duk dan Kano da ya cancanta ya yi rajistar zabe, ya yi.
Mambobin kwamitin sun hada da kwamishiniyar harkokin mata, yara da nakasassu, Hajiya Amina Abdullahi; Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, mai ba da shawara na musamman kan jama’a, mai ba da shawara na musamman kan harkokin dalibai, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa, mai ba da shawara na musamman kan harkokin jam’iyyu, Darakta Janar, da kuma Manajan Daraktan Kamfanin Rediyon Jihar Kano.
Sauran sun hada da wakilan kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), kungiyat ‘yan kwadago ta Nijeriya (NLC), shugabar kungiyar kananan hukumomin Nijeriya (ALGON), hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), ‘yan kasuwa da wakilan kungiyoyin taimakon kai-da-kai da jama’a da dai sauransu.
A yayin da take kira ga masu ruwa da tsaki da sauran al’umma da su hada kai da gwamnati wajen cimma wannan muhimmin buri, sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, rajistar masu kada kuri’a, hakki ne na jama’a da ke taimakawa wajen tsara makomar gudanar da mulki a jihar da kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp