Fitaccen fasto a Jihar Kaduna mai gabatar da wa’azi a Cocin Christ Evangelical and life Intercessory Ministry da ke a anguwar Sabon Tasha Yohanna Buu, ya raba buhun hatsi ga Musulmai mabukata na musaman sama da 1,000 da ke jihar domin su ji dadin yin azumin watan Ramadan na bana.
Buru ya rabar da kayan ne ga masu bukata ta musamman da ke kan titin Kano, inda ya ce, rabar da kayan ya zama wajibi idan aka yi la’akari tsadar kayan masarufi da ke fuskanta a jihar.
- Hukumar Leken Asiri Ta Amurka Ta Sake Tabka Karya Kan Batun “Nord Stream”
- An Yanke Wa Wasu Mutane 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Legas
A cewarsa, musulmai masu bukata ta musamman sama da 1000 muke son mu rabarwa da buhunhun masara da gero, inda ya ce, a azumin bara, mun rabar masu da buhunhun amasara, shinkafa da sauran kayan abinci.
Ya ce, a rabon na wannan shekarar, mun hada har da butocin yin sallah da tabarmi, musamman don su yi amfani da su wajen yin sallah da yin addu’oin Allah ya kawo karshen kalubalen rashin tsaro da kasar nan, musamman arewacin kasar ke fuskanta.
Buru ya ce, mahimmancin rabar da kayan shine don a kara karfafa dankon zumunci a tsakanin musulmai da mabiya addinin kiritsa da ke a cikin jihar.
Faston ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da ke jihar da su yi amfani da dukiyoyin su, musamman don ciyar da masu bukata ta musamman da kuma sauran marasa galihu a cikin wannan watan na Ramadan.
Ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa, musamman masu sayar da kayan masarufi da su guji kara farashin don cin kazamar riba a cikin watan na Ramadan.
Daya daga cikin jagororin masu bukata ta musamman da ya karbi kayan a madadin sauran ‘yan uwansa mallan Hassan Lawal Mohammed sarkin kutaren ya mika godiyar su bisa ga tallafin, inda ya ce, yau kimanin shekaru goma kenan Buru na kawo masu irin wannan tallafin.
Bugu da kari wasu makarantun tsangaya da kuma wasu kafafen yada labarai a jihar suma sun amfana da wannan tagomashin na fasto Buru.