Yayin da ake shirye shiryen shigowar watan azumin Ramadan, hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta jihar Kano, ta bada umarnin kulle dukkannin gidajen Galar da ke fadin jihar.
Wannan na zuwa ne biyo bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin kungiyar masu gidajen gala reshen jihar Kano a ofishinsa.
- Ina Da Burin Ganin Mata Sun Dogara Da Kansu A Harkokin Rayuwa – Lu’ayyat Mu’az
- Arsenal Ta Hau Kan Teburin Firimiya Bayan Da Ta Doke Brentford A Emirates
A cewar shugaban Hukumar, Abba El-mustapha, dokar zata fara aiki ne tun daga ranar Lahadi 10 ga wata Maris, har zuwa 1 ga watan shawwal wato ranar bikin karamar sallah.
Abba El-mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji karya doka domin duk wanda hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar, to hakika zata dauki tsatstsauran mataki a kansa wanda ka iya sawa ya rasa lasisinsa na gudanarwa.