Sanata Abdul’Aziz Yari (APC-Zamfara), ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Ramadan wajen yi wa Shugaba Bola Tinubu addu’a, domin daidaita tsaro da tattalin arzikin kasa.
Shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar siyasar Yari, Ibrahim Muhammad, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Lahadi.
- Ramadan: Sanata Abdulaziz Yari Zai Raba Tirela 358 Na Kayan Abinci A Jihar Zamfara
- Ramadan: Sanata Yari Ya Gwangwaje Magidanta 250,000 Da Tallafin Abinci A Zamfara
Yari wanda tsohon gwamnan Zamfara ne a halin yanzu yana wakiltar mazabar Zamfara ta yamma a majalisar dokokin kasar.
Mohammad Yari, ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu ‘ya’yan jam’iyyar (APC), wadanda suka fito daga mazabun siyasa 147 da ke fadin kananan hukumomin jihar 14, a gidansa da ke Talata Mafara.
Ya ce Musulunci ya umarci mabiyansa da su rika yi wa shugabanninsu addu’a domin samun nasara, “saboda su (shugabannin) ne suke tafiyar da rayuwar mabiyansu.
Dan majalisar ya ce al’ummar kasa da shugabanninta na bukatar addu’a daga kowa da kowa.
Yari ya bayar da gudummawar Naira 50,000 ga kowane mutum su 2,500 da za su halarci shirin na Ramadan a makon d ya gabata da tufafi guda daya gabanin bikin Sallah.