Yayin da aka shiga watan Ramadan mai alfarma, ‘yan kasuwa a Kano na ci gaba da kokawa kan rashin samun kwastomomi don yin sayayyar kayayyaki.
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suka zanta da manema labarai ranar Lahadi a Kano, sun danganta lamarin da karancin samun kwastomomi.
- Ramadan: Tinubu Ya Buƙaci Mawadata Da Su Taimakawa Mabuƙata
- An Kaddamar Da Kasuwar Baje Kolin Watan Ramadan A Kano
Wani mai sayar da kayan abinci, Malam Tanko Idris, ya ce idan aka kwatanta da shekarun baya, cin kasuwa ya ragu a bana.
Idris ya ce duk da cewa farashin wasu kayayyaki, musamman kayan masarufi yakan yi tashin gwauron zabi a lokacin azumin watan Ramadan, amma har yanzu mutane sukan yi sayayyar kayan.
Shi ma wani dan kasuwa mai suna, Saminu Dauda, ya koka da yadda harkokin kasuwanci ba sa tafiya sosai kamar a baya.
Ya bayyana cewa tabarbarewar tattalin arziki a kasar ya taimaka wajen samun kai a wannan yanayi.
Wani mai sayar da kayan lambu, Sani Ali, ya koka kan cewa lamarin ya ba shi mamaki idan aka kwatanta da abin da ya saba gani a kasuwa a duk lokacin da watan Ramadan ke gabatowa ko kuma ya fara.
Ali ya ce kwastomomi da dama sun koka da karancin kudade saboda yanayin tattalin arziki.
Ya kuma koka da yadda yanayin tattalin arziki ya shafi ciniki da kwastomomi da dama.
Wani kwastoma, Nura Baba, ya koka da tsadar shinkafa da gero da fulawa da kuma sukari, wanda a cewarsa ya ce abun yana damunsa musanman a lokacin azumi.
“Misali, ana sayar da sukari sama da Naira 5,5000 kan kowanne mudu, shinkafa ana sayar da ita sama da Naira 3,500, ana sayar da gero kan Naira 1,800 kan kowane mudu, da farashin kwai kan Naira 3,300, ta yaya suke so mu ciyar da azumin Ramadan?”
Ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da ma su sayar da kayan abinci a jihar da su rage farashinsu a cikin wata mai alfarma.