Rundunar ‘yansanda reshen jihar Kano ta bukaci al’ummar musulmi da su kasance masu taka-tsan-tsan a yayin gudanar da ayyukan ibada na yau da kullum a watan Ramadan a sassan jihar.
Kwamishinan ‘yansandan, Usaini Gumel, ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema Labarai a Kano ranar Litinin.
- Ramadan: ‘Yan Kasuwa Sun Koka Kan Samun Ƙarancin Ciniki A Kano
- Ramadan: Tinubu Ya Buƙaci Mawadata Da Su Taimakawa Mabuƙata
Gumel ya ce, rundunar ta samar da tsare-tsaren tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Hukumar ta umurci kowa da kowa da ya yi taka tsantsan yayin da ake gudanar da sallar magariba (Tarawi) da lokacin halartar wuraren tafsirin da kuma sallar dare (Tahajjud) a jihar,” Cewarsa.
Ya kuma yi kira ga mazauna garin da su kai rahoton duk wadanda suke zargi da wani abu na rashin gaskiya zuwa wurin ‘yan sanda mafi kusa domin daukar matakan tsaro cikin gaggawa.
Kwamishinan ya shawarci al’ummar Musulmi da su tabbatar da sanya ido sosai a gidajensu da yayin da suke tafiya zuwa Masallatai.
“A dangane da haka, rundunar ta bukaci al’ummar Jihar Kano da su ba jami’an tsaro hadin kai, su kasance masu bin doka da oda da bin ka’idojin hanya da sauran muhimman ka’idoji don gujewa tabarbarewar zaman lafiya.