Babban sakataren majalisar dinkin duniya MDD, Antonio Gutteres, acikin jawabinsa na ranar kawar da talauci ta Duniya, ya yi ikirarin cewa, a wannan duniyar ta mu mai cike da dimbin arziki, bai kamata Talauci ya yi ma ta katutu ba.
Gutteres ya ce, duk da dimbin arzikin cikin duniyarmu amma kusan mutane miliyan 700 ke fama da kalubalen rayuwa, inda suke rayuwa a kasa da dala 2.15 daidai da naira N2,000 a duk rana.
- Ranar Abinci Ta Duniya: Gwamnatin Kaduna Za Ta Samar Da Tsaftataccen Ruwa Da Abinci Mai Gina Jiki
- Gwamna Uba Sani Ya Nada Dakta Mayere Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna
Sama da mutane biliyan daya ne ke fama da matsananciyar rayuwa daga karancin abinci, ruwa, lafiya da ilimi.
Akwai biliyoyin mutanebda ba su da tsaftataccen muhalli, ayyukan yi, wurin kwana ballanta kuma samun ‘yancin zamantakewa.
A halin yanzu, duniyarmu tana fama da rikice-rikicen yaki, rikicin wariya na kara kamari – musamman kan mata da ‘yan mata.
Duk abubuwan da suka janyo koma baya ga ci gaban mu da tsanancin talauci, na da alaka da tsarin tafiyar da harkokin kudi na duniya wanda ya tsufa da kuma rashin adalci wanda ke hana kasashe masu tasowa tallafawa don kawar da talauci da cimma manufar shirin ‘yancin zamantakewa da kawar da talauci na MDD (SDGs).
Kusan mutane miliyan 500 ne za su kasance cikin matsanancin talauci acikin 2030. Wannan, sam ba a abin da za a sa ido ana kallo ba ne kawai, dole a yi wani abu.
A taron koli na SDG da aka yi a watan Satumba, shugabannin kasashen duniya sun amince da bukatar yin garambawul ga tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa, tare da himmatuwa wajen yin wani kwakkwaran shiri don ceto muradun ci gaba mai dorewa da kuma kara kaimi wajen kawar da talauci a ko’ina.
Wannan ya hada da bayar da tallafi don karfafa shirin SDG na akalla dala biliyan 500 a kowace shekara.
Shugabannin sun kuma amince da matakin da aka dauka da niyyar kawar da talauci da wahalhalun rayuwa ga dukkan mutane – daga tsarin samar da abinci da ilimi zuwa ayyukan yi masu nagarta da fadada kariyar zamantakewa.