• English
  • Business News
Friday, August 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ranar Hausa: Masana Sun Bayyana Bunkasa Da Tasirin Harshen A Duniya

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto and Sulaiman
8 hours ago
in Manyan Labarai
0
Ranar Hausa: Masana Sun Bayyana Bunkasa Da Tasirin Harshen A Duniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tarihi da mabiya tarihi sun tabbatar da girma, kima da daukakar harshen Hausa a idon duniya ya daidaita da duk wani harshe da ake da shi a doron kasa.

A bayyane yake cewar inma harshen Hausa a matsayin harshe, adabi da al’adun Hausawa sun shiga kowace nahiya ta duniya tare da kyankyashe ‘ya’ya da jikoki.

  • Me Ya Sa Wasu Kafofin Watsa Labarun Japan Suke Kokarin Musanta Kisan Kiyashin Nanjing?
  • An Bude Bikin Nune-Nune Na Masana’antar Manyan Bayanai Ta Big Data A Kudu Maso Yammacin Sin

Karbuwa da bunkasar Harshen Hausa a matsayin Harshe mafi girma a Afurka ta Yamma ne dalilin da ya sa al’ummar Hausa da Hausawa ke karrama harshen ta hanyar shirya bukin tunawa da harshen a kowace shekara.

A yau harshen Hausa ya bi sahun harsuna dubu 7500 da ake da su a duniya da al’ummar su ke bukin tunawa da harsunan a kowace shekara a bayyane ko akasin hakan.

A shekaru 10 sa suka gabata ne daya daga cikin zaratan matasan Hausawa mai kishin Hausa da son ci- gaban ta a kasar Hausa ya jagoranci kirkirar ranar Hausa ta duniya a kafafen sada zumunta na zamani domin jin amon Hausawa da al’adun su.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnan Kebbi Ya NaÉ—a Sanusi Mika’ilu Sami A Matsayin Sabon Sarkin Zuru 

Gwamnatin Bauchi Ta Amince Da N32,000 A Matsayin Mafi Karancin KuÉ—in Fansho

Harshen Hausa shine kan gaba a yawan masu magana a Afrika ta Yamma ta yadda yake da karbuwa a Nijeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Benin, Gabon, Togo, Afrika ta Tsakiya, Sudan da Saudiyya da sauran su. Hasalima kowace nahiya ta duniya akwai jami’ar da ake koyar da harshen Hausa da Hausanci.

Bunkasar Harshen Hausa ya sa harshen ke barazanar batar da kananam harsuna wadanda tuni wasu da dama a yau suka bace ba amo ba labarin su a bisa ga yadda yake mamaye harsuna a mabambantan kasashe.

Sai dai duk da kima da martabar da Harshen Hausa yake da shi da yadda daruruwan miliyoyin al’umma ke magana da Harshen har yau Jamhuriyar Nijar kadai ce kasar da ke amfani da Hausa a hukumance a matsayin harshen kasa.

Farfesan al’adun Hausawa na farko a duniya (2009) Aliyu Muhammad Bunza ya ce a na gudanar da taron ranar Hausa ta duniya domin jin amon Hausawa da al’adun su da gudunmuwar da suka bayar a duniyar zamanin su domin sun mamaye kasashe da yawa a Afrika sun kuma kafa sansani da yawa.

Shehin Malamin wanda ke koyarwa a jami’ar Usmanu Danfodoyo da ke Sakkwato ya kuma ce manufar taron shine domin Hausawa su san ina aka kwana ina aka tashi, samun hadin kan su a duk inda suke da wadanda ke a kasar Hausa da wajen kasar Hausa.

A bana a ranar 26 ga Agusta ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar Hausa ta duniya an gudanar da gagarumin bukin ne a Daura da ke jihar Katsina a hamshakiyar fitacciyar masarautar da ta kafa ingantaccen tarihin zama tushen Hausa da Hausawa, tarihin da babu wata kasa a kasar Hausa da ke da irin sa.

Basarake mai magana daya da murya daya, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, kasaitaccen Sarkin da ya yi fice wajen daga darajar Hausawa da al’adunsu tare da gudanar da mulkin gaskiya da adalci ne ya karbi bakuncin dubun- dubatar al’ummar ciki da wajen kasar Hausa da suka halarci taron

Taron ranar Hausa na bana a Daura wanda shine karo na 10 an yi masa taken “Amfani da Harshen Hausa wajen wanzar da zaman lafiyya” ya kayatar da da jama’a musamman yadda Hausa da Hausawa suka hadu, suka raya harshen, baje kolin al’adunsu su, tattauna matsaloli da kalubalen da harshen ke fuskanta da hanyoyin magance su.

A taron an gudanar da kayataccin wasannin Hausawa da suka yi fice da su, kama daga hawan daba tsakanin kasashen Hausa Bakwai da na Kanne Bakwai da kokawa da wasannin wuta na makere, haka ma mawaka sun baje fasahar hikimar su.

Abdulbaki Jari, matashin da ya jagoranci assasa ranar Hausa ta duniya ya bayyana cewar ba wai ana tunawa da ranar Hausa kadai a Afrika ta Yamma da Afrika ta Tsakiya ba, har ma a wurare da dama na duniya ciki har da Turai, Amurka da Asiya.

Dan jaridar ya bayyana cewar Harshen zai kai matakin da ya kamata a duniya idan har masu amfani da harshen suka hada kai domin magance kalubalen da ya dabaibaye harshen.

A kan gudanar da taron a Daura kuwa, Jari ya bayyana cewar Daura ita ce tushen Hausa kuma cibiyar dukkanin kasashen Hausa wadda ke martabawa, mutuntawa da daga dajar al’adun Hausawa don haka ta ke da kima a wajen Hausawa.

Jari ya ce ba wai sun assasa taron domin a rika gudanar da buki ba kawai, a’a, ya ce hanya ce da Hausa da Hausawa a fadin duniya za su hada kai su tattauna kalubalen da ke damun su da samar da zaman lafiya mai dorewa.

Matashin ya bayyana cewar harshen Hausa yana da girma da daukaka, don haka ya bambanta da sauran harsunan da ke bacewa, ya ce a na magana da harshen a nahiyar Afrika tsakanin mutane fiye da miliyan 170.

Jari wanda ma’aikaci ne a kafar yada labarai ta TRT Afrika ya bayyana cewar Harshen ya riga ya samu gurbi a kasashen Afurka musamman a Jamhuriyar Nijar a inda ya ce sama da kaso 80 cikin 100 na al’ummar kasar suna magana ne da Hausa. Haka ma a Ghana suna da amfani da Hausa sosai.

Ya ce girman harshen Hausa da karbuwar sa a duniya ne ya sa kafafen yada labarai da dama a fadin duniya ke yada shirye- shiryen su da Hausa domin isar da sako ga dinbin mabiyan su a fadin duniyar Hausawa.

Matashin ya bayyana cewar kamar wasa suka assasa ranar Hausa ta duniya a 2015, a kafafen sada zumunta amma ba zato ba tsammani saboda karbuwa da tasirin harshen, a yanzu duk duniya a na maganar tare da gudanar da taron a kasashe kusan 25.

Jari wanda ya kafa ingantaccen tarihi a kasar Hausa ya gabatar da bukatar da ke ci wa Hausawa tuwo a kwarya ta hanyar yin kira ga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma wato ECOWAS da ta duba yiyuwar sanya harshen Hausa a cikin harsunan da ake harkokin kasuwanci da shi da mu’amalar zamantakewa a hukumance a yankin wanda hakan zai kara taimakawa harshen da daga darajar harshen a idon duniya.

A tsokacinsa kan muhimmiyar ranar da tasirin ta, Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya bayyana cewar Hausawa na gudanar da bukin ranar Hausawa ta duniya ne domin bunkasa harshen tare da kokarin ganin ya zama daya daga cikin harsunan da ake koyar da ilimi da shi kamar yadda ake koyar da larabci, Turanci, Asiyanchi da Faransanchi da sauransu.

Farfesan ya bayyana cewar mashirya taron na son ganin Harshen Hausa ya kai matsayin da za a rika koyar da kowane irin limin duniya da shi.

A kan yadda za a inganta harshen kuwa, Bunza ya ce a yi kokarin samar mashi mazauna daga makarantun furamari, sakandire zuwa jami’o’i ya zama harshen hukuma a wajen da Hausawa suka rinjaye mutane.

Malamin ya bayyana cewar idan aka mayar da kowane ilimi a cikin harshen Uwa to ba yadda za a yi a rinjaye shi a harkokin ilimi da tsaro.

A cewar sa, Shehin Malamin Malamai, marigayi Farfesa Mahadi Adamu a 1975 ya yi rubutun musamman kan gudunmuwar Hausawa a tarihin Afrika ta Yamma kuma ba a samu wata al’umma da aka yi bayanin gudunmuwar ta ba kamar Hausawa da suka mamaye wuraren.

Ya ce taron ranar Hausa na da manufar hadin kan Bahaushe, sanin ina Bahaushe ya fito, yadda al’adunsa kyawawa suke, tabbatar da harshen Hausa da bunkasar sa da kokarin inganta Hausa da Hausawa da kara masu kwarin guiwa ga ci- gaban zamani.

Farfesa Bunza ya bayyana cewar ba a san adadin Hausawa da ake haihuwa da wadanda ke mutuwa ba don haka fadin adadin su abu ne mai wahala.

Ya ce a shekarar 2020 an bayyana cewar akwai Hausawa akalla miliyan 150 wanda ya ce adadin ba daidai ba ne domin adadin ya baiwa Hausa matsayin Harshe na 11 a duniya a cikin harsuna 7500.

Ya ce “idan aka bi adadin kwarai Hausa ta na da akalla adadin mutane miliyan 300 a duniya tare da zama harshe na hudu ko na biyar da ake jin sa a duniya saboda duk duniya a bakar fata da turai babu mai auren mace hudu in ba Bahaushe ba, ya fi su iyali da mata, haka ma a Afrika babu al’umma mafi harkokin kasuwanci irin Hausawa.”

A jawabinsa Firamin Ministan Jamhuriyar Nijar, Muhammad Lamine Zain ya bayyana cewar taron ya kara tabbatarwa duniya cewar Nijeriya da Nijar abu daya ne, ya ce suna fatar taron zai taimaka wajen warware matsalar diflomasiyya da ke akwai tsakanin kasashen biyu.

Gwamnan soji daga Jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, Kanal Muhammad Sani masallatchi wanda ya wakilci Firayim Ministan bayyana cewar yadda Hausa da Hausawa suka hadu domin bunkasa harshen su ya nuna tasirin da harshen yake da shi a duniya.

Firayim Ministan ya bayyana cewar taron zai kara hada kan Hausawa a ko’ina suke a duniya a matsayin ‘yan uwa daya al’umma daya. Haka ma Sarkin Musulmin Damagaram Aboubacar Oumarou Sanda ya albarkaci taron da kakkarfar tawaga.

Duk da kalubalen bacewar wasu kalmomi da harshen ke fuskanta, yadda dubun- dubatar al’umma a kasar Hausa suka rungumi ranar Hausa ta duniya tare da tunawa da ranar ya nuna kima da tasirin harshen da yadda yake kara bunkasa a idanun duniya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Me Ya Sa Wasu Kafofin Watsa Labarun Japan Suke Kokarin Musanta Kisan Kiyashin Nanjing?

Next Post

Tinubu Ya Umarci A Yi Bincike Kan Hatsarin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna

Related

Gwamnan Kebbi Ya NaÉ—a Sanusi Mika’ilu Sami A Matsayin Sabon Sarkin Zuru 
Manyan Labarai

Gwamnan Kebbi Ya NaÉ—a Sanusi Mika’ilu Sami A Matsayin Sabon Sarkin Zuru 

20 hours ago
Gwamnatin Bauchi Ta Amince Da N32,000 A Matsayin Mafi Karancin KuÉ—in Fansho
Manyan Labarai

Gwamnatin Bauchi Ta Amince Da N32,000 A Matsayin Mafi Karancin KuÉ—in Fansho

22 hours ago
Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000
Manyan Labarai

Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000

24 hours ago
Dangote Zai Gina Kamfanin Taki A Habasha Kan Dala Biliyan $2.5
Tattalin Arziki

Dangote Zai Gina Kamfanin Taki A Habasha Kan Dala Biliyan $2.5

1 day ago
An Kama Matasa 2 Kan Nuna Makamai A Shafukan Sada Zumunta A Kano
Manyan Labarai

An Kama Matasa 2 Kan Nuna Makamai A Shafukan Sada Zumunta A Kano

1 day ago
ADC Tana Da Damar Kayar Da Tinubu A ZaÉ“en 2027 – Amaechi
Manyan Labarai

ADC Tana Da Damar Kayar Da Tinubu A ZaÉ“en 2027 – Amaechi

1 day ago
Next Post
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Tinubu Ya Umarci A Yi Bincike Kan Hatsarin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Zartar Da Dokar Karya Farashin Magunguna 

Bincike Ya Nuna Tarin Fuka Na Kashe Mutum 71,000 A Nijeriya Duk Shekara

August 29, 2025
Al’umma Da Ƴan Bindiga Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Katsina

Al’umma Da Ƴan Bindiga Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Katsina

August 29, 2025
Peter Obi Ya Caccaki Gwamnati Kan Ƙarin Kuɗin Fasfo

Peter Obi Ya Caccaki Gwamnati Kan Ƙarin Kuɗin Fasfo

August 29, 2025
Yaya Da Kani Sun Mutu A Cikin Ramin Masai A Kano

Yadda Aka Gudanar Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Kano

August 29, 2025
Yadda Aka Gudanar Da Taron Ranar Hausa Ta Duniya A Masarautar Daura

Yadda Aka Gudanar Da Taron Ranar Hausa Ta Duniya A Masarautar Daura

August 29, 2025
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna

A Daina Gaggawar Murnar Samun Nasara Kan Ta’addanci A Nijeriya

August 29, 2025
Kyawawan Abubuwa Da Allah Ya Yi Wa Manzon Allah (SAW) Na Girmamawa

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah

August 29, 2025
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Tinubu Ya Umarci A Yi Bincike Kan Hatsarin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna

August 29, 2025
Ranar Hausa: Masana Sun Bayyana Bunkasa Da Tasirin Harshen A Duniya

Ranar Hausa: Masana Sun Bayyana Bunkasa Da Tasirin Harshen A Duniya

August 29, 2025
Me Ya Sa Wasu Kafofin Watsa Labarun Japan Suke Kokarin Musanta Kisan Kiyashin Nanjing?

Me Ya Sa Wasu Kafofin Watsa Labarun Japan Suke Kokarin Musanta Kisan Kiyashin Nanjing?

August 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.