Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga gidajen rediyo a faɗin Nijeriya da su yi amfani da kafafen su wajen ilimantar da jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa.
A cikin wata sanarwa da ya bayar domin bikin Ranar Rediyo ta Duniya ta 2025, wadda ake gudanarwa a duk shekara a ranar 13 ga Fabrairu (yau kenan), Idris ya jaddada muhimmancin rediyo wajen wayar da kan al’umma da kuma ƙarfafa su don ɗaukar matakan da za su daƙile matsalar sauyin yanayi.
- Maryam Malika Ta Buƙaci Kotu Ta Tabbatar Da Sakin Da Mijinta Yayi Mata
- Ya Kamata Amurka Ta San Ana Barin Halal Don Kunya
Taken ranar ta bana, wato “Rediyo da Sauyin Yanayi,” yana nuni da buƙatar gaggawa na ɗaukar matakan magance matsalolin muhalli da ke shafar Nijeriya da duniya baki ɗaya.
A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli.
“A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.”
Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron COP29 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na ƙasar Azerbaijan inda Shugaban Ƙasar ya yi bayanin yadda Nijeriya take fama da matsalar sauyin yanayi da matakan da gwamnati ke ɗauka don rage fitar da hayaƙin da ke dagula yanayi, ƙarfafa juriya, da shigar da hanyoyin magance matsalar cikin tsare-tsaren ƙasa.
Idris ya yi kira ga gidajen rediyo a Nijeriya da su gabatar da shiryayyun bayanai da ilimantarwa kan sauyin yanayi, su haɗa kai da masana, da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin isar da ingantattun bayanai ga jama’a.
Ya ce: “Ta hanyar shirye-shiryen ilimantarwa da bayanai, za mu iya bai wa al’umma ilimi da kayan aiki da za su taimaka masu wajen daidaita kan su da sauyin yanayi da kuma rage tasirin sa.
“Haka nan, yana da matuƙar muhimmanci ga gidajen rediyo su haɗa kai da ƙungiyoyi da masana a fannin sauyin yanayi don samar da ingantattun bayanai ga masu sauraro.
“Ta hanyar tattaunawa da masana kimiyya, da ƙwararru a fannin muhalli, da masu tsara manufofi, za mu ƙarfafa fahimtar mu game da wannan matsala tare da nemo hanyoyin magance ta, bisa la’akari da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
Ministan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su duba halayen su na yau da kullum da kuma yin ƙananan canje-canje domin yaƙi da sauyin yanayi, kamar rage amfani da robobi, rage amfani da makamashi ko wutar lantarki, da haɓaka noma mai ɗorewa.
Har ila yau, ya jaddada cewa matsalar sauyin yanayi ba ta tsaya a wata ƙasa kaɗai ba kuma tana buƙatar haɗin gwiwar ƙasashe daban-daban don samar da mafita mai ɗorewa.
Yayin da yake taya UNESCO murna bisa ƙirƙirar Ranar Rediyo ta Duniya, Idris ya tabbatar da cewa gwamnati tana da niyyar amfani da rediyo don kawo sauyi mai kyau a cikin al’umma.
Ya ce: “Mu yi amfani da ƙarfin rediyo don kawo sauyi mai kyau a cikin al’ummomin mu da kuma yaƙi da mummunan tasirin sauyin yanayi.
“Ta hanyar haɗin gwiwa da himma tare, za mu iya gina Nijeriya mai ɗorewa da juriya.
“A wannan rana ta Ranar Rediyo ta Duniya, mu yi alƙawarin kawo sauyi da kare duniyar mu domin amfanin zuriyar da ke tafe.”