Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya horaswa ta musamman ga ‘yan jarida daga ɓangarori daban-daban a kan muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa domin taimaka wa wayar da kan jama’a game da abubuwan da ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwa da yadda za a magance su ko a rage kaifinsu.
A yayin horaswar masana daban-daban sun gabatar da ƙasidu da suka yi bayani game da ‘yancin Ɗan’adam wajen samun kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa da muhimmancin abin da matakan riga-kafin kamuwa da cututtukan da suka shafi ƙwaƙwalwa.
- Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada ‘Yancin Dan Adam Wajen Samun Kiwon Lafiyar Kwakwalwa
- Kisan Dan Jarida: ‘Yansandan Sun Kama Wadanda ake Zargi Da Hannu A Zamfara
Bugu da ƙari an horas da ‘yan jaridan a kan alaƙar aikinsu da kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa da yadda ya kamata su riƙa bayar da rahotannin da suka shafi kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa cikin ƙwarewa da tausayawa.
Wakazalika, an aiwatar da wasu tsare-tsare na gwajin lafiyar ƙwaƙwalwar mahalartan domin kowa ya san matsayinsa da irin matakan da suka kamata mutum ya ɗauka domin daidaita rayuwarsa ta yadda ba za ta haifar masa da matsalar ƙwaƙwalwa ba.
An fara gabatar da bikin ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ne a ranar 10 ga watan Oktobar 1992 ta hannun Ƙungiyar Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Duniya bisa goyon bayan Hukumar Lafiya ta Duniya da sauransu.
A saƙonsa na bikin ranar ta bana, Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana cewa, lafiyar ƙwaƙwalwa da tunani mai kyau yana ba Ɗan’adam damar gudanar da rayuwa mai gamsarwa da ba da gudummawa sosai ga al’ummomi.
Ya nuna takaicinta cewa, daya cikin mutane takwas a duniya na fama da matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa, wanda hakan ya fi ƙamari cikin ‘yan mata da matasa.
Bugu da ƙari, mutum uku cikin mutane huɗu da ke fama da matsalar ƙwaƙwalwa, ba su samun isasshiyar kulawa ko kuma babu kulawa ma kwata-kwata, sannan da yawa suna fuskantar ƙyama da wariya a cikin al’umma.
“Kiyaye Lafiyar ƙwaƙwalwa ba gata ba ce ta wane da wane, haƙƙi ce ta dukkan Ɗan’adam– ya zama dole a kula da Lafiyar ƙwaƙwalwa a duk cikin al’ummatai da ke cikin faɗin duniyarmu. Dole ne gwamnatoci su ba da kulawa don magani ga masu matsalar ƙwaƙwalwa da kuma kiyaye hakkinsu.
“Dole ne kuma a magance matsalar cin zarafi tare da karya duk wani shingen da ke hana mutane neman tallafi don magance matsalar ƙwaƙwalwa kuma dole ne mu magance matsalar ƙwaƙwalwa tun daga tushe musamman ta fuskar talauci, wariya, tashin hankali da sauransu.
“A wannan rana ta kula da Kiwon Lafiyar Hankali ta Duniya, muna sake jaddada cewa, kiyaye lafiyar ƙwaƙwalwa, hakki ce kuma ‘yancin Ɗan’adam ne ba tare da nuna wata wariya ba, tare za mu gina duniya mafi ƙoshin lafiya inda kowa zai yi alfahari da ita” in ji ji sakataren majalisar.
Wata ƙididdiga da wata ƙwararriyar da ta yi lacca a taron horas da ‘yan jaridar, Mrs. Moji Makanjuola ta bayyana, ta nunar da cewa akwai ‘Yan Nijeriya aƙalla miliyan 20 da ke fama da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa, sannan du-du-du asibitocin da ke kula da masu matsalar ƙwaƙwalwa na gwamnati ba su wuce guda takwas ba, da na masu zaman kansu guda 30, kana likitocin ƙwaƙwalwa 350 ne kacal ake da su a duk faɗin Nijeriya.