• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ranar Ma’aikata: Bayan Cike Giɓin Albashin Da Muka Gada, Za Mu Ci Gaba Da Inganta Walwalar Ma’aikata – Gwamnan Zamfara

byLeadership Hausa
1 year ago
Ma'aikata

A wani ɓangare na bikin ranar ma’aikata ta bana, Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta inganta rayuwar ma’aikatan jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne wurin ggagarumin bikin ranar wanda aka saba gudanarwa a duk faɗin ƙasar nan a kowace ranar 1 ga Mayu, wanda na jihar ya gudana a Sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau a yau Laraba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta na nan a kan bakar ta na tafiya tare da ma’aikatan a duk harkokin mulkin jihar.

  • IPMAN Ta Yi Barazanar Rufe Gidajen Mai Sama Da 30,000 Saboda Bashi

Sanarwar ta Sulaiman Bala ta ƙara da cewa, a jawabin Gwamnan ga ma’aikata, ya yi alƙawarin aiwatar da tsare-tsaren sa guda shida da ya tsara don haƙƙaƙa shirinsa na tsamo jijar Zamfara daga halin da ya same ta.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

“Gwamnatina ta yi na’am da muhimmiyar rawar da ma’aikata ke takawa wajen ƙaddamar da ayyuka da aiwatar da manufofin gwamnati. Ma’aikata da gwamnatoci abokan haɗin gwiwa ne wajen aiwatar da ayyukan ci gaban al’ummarmu.

“Ma’aikata ne ke taimaka wa gwamnati wajen cimma burinta na samar da ayyuka ga jama’a. Bisa la’akari da haka, za mu ci gaba da lalubo hanyoyin inganta jin daɗin ku da na iyalanku, musamman idan aka yi la’akari da irin matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu sakamakon cire tallafin man fetur da manufofin kuɗi da ya haifar da koma-baya a darajar Naira da hauhawar farashin kayayyaki da ba a taɓa ganin irinsa ba a ƙasar nan.”

Ma'aikata

Gwamnan ya kuma bayyana wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin watanni goma sha ɗaya na farko a kan karagar mulki.

“Ya ku ’yan uwana, ina mai farin cikin bayyana cewa a cikin watanni goma sha ɗaya da kafa gwamnatinmu, ma’aikata a Jihar Zamfara suna jin daɗi. Mun fara ta hanyar kawar da giɓin albashin da muka gada tare da tabbatar da biyan albashin akan lokaci, tare da tsawaita wasu abubuwan jin daɗin rayuwar ma’aikata.

“Don ci gaba da wannan yunƙuri, gwamnati ta aiwatar da hanyoyin da za a tabbatar da cewa ma’aikata na gaske ne kaɗai ke cin gajiyar albashinmu. Har ila yau, muna tuntuɓar ma’aikata kan batun albashi, bisa la’akari da yadda rayuwa take a yau. Ina yaba wa da goyon bayan da gwamnatina ke bayarwa da kuma dangantakar da ke tsakaninta da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a jihar. Haƙiƙa yana ɗaya daga cikin nasarorin da ake samu na ci gaba wajen maido da inganta harkokin gwamnati.

Bugu da ƙari, Gwamnan na Jihar Zamfara ya yi alƙawarin daidaita dukkan ayyukan gwamnati da kuma gyara ayyukan ma’aikatan gwamnati domin ɗaukar salon gudanar da harkokin gwamnati na zamani.

“Don inganta harkokin gwamnati, nan ba da jimawa ba za mu bayyana tsare-tsaren mu na zamanantar da duk ayyukan gwamnati da kuma sake fasalin ma’aikatan, don aiwatar da tsarin tafiyar da harkokin gwamnati na zamani.

“Wannan zai haɗa da sabbin hanyoyin tantance ayyukan ma’aikata, horarwa da tabbatar da ƙwarewarsu a tsakanin wasu tsare-tsare da dama.

Ma'aikata

“Hakazalika, gwamnati ta ƙuduri aniyar hana zamba da wasu munanan ɗabi’un da suke gurɓata ayyukan gwamnati.

“Saboda sadaukarwar da ma’aikata suka yi a lokacin hidimarsu, ya dace a riƙa girmama su da mutunta su. Wannan ne ya sa muka ɗauki matakin biyan bashin garatuti da gwamnatinmu ta gada. Da zarar mun kawar da basukan, za mu tabbatar da biyan duk waɗanda suka yi ritaya daga ayyukan gwamnati da na ƙananan hukumomi cikin gaggawa.

Ma'aikata

“Da wannan aiki, In Sha Allahu, ma’aikata ba za su sake samun wani dalilin da zai sa su ji shakkar yin ritaya ba, wanda yakan haifar da kwaɗayin ci gaba da aiki.” In ji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Next Post
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2

Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda, Sun Ceto Mutane A Katsina Da Filato

LABARAI MASU NASABA

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version