Masu hikimar magana na cewa, “ilmi gishirin zaman duniya. Ko shakka babu, ilmi shi ne jigon rayuwa, kuma ta hanyar ilmi ne ake samun ci gaba wanda ke shafar rayuwar bil adama daga dukkan fannoni.
Ranar malamai ko kuma “Teacher’s Day” a Turance, rana ce da ake kebe wa don tunawa da kuma yin nazari game da irin rawar da malamai suka taka ko suke takawa, matsalolinsu, nasarorin da suka cimma, gami da nuna musu yabo bisa gagarumar gudummawar da suke bayarwa a bangaren ilimi wanda shi ne ginshikin rayuwa da ci gaban duniya.
Kowace kasa tana da ranar da ta kebe don murnar wannan rana inda a wasu kasashe da yankuna a kan shirya shagulgulan a wannan rana mai matukar muhimmanci.
A nan kasar Sin, an kebe ranar 10 ga watan Satumbar kowace shekara a matsayin Ranar Malamai ta kasa. Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya taba bukatar malamai da su sadaukar da kai ga ayyukansu, ta yadda za a daga martabar ilimi a sassan kasar baki daya.
Xi ya kuma bukaci kusoshin JKS da hukumomin gwamnatoci a dukkan matakai, da su daukaka aikin koyarwa ko malanta ta yadda sana’ar za ta samu kimar da ta dace. (Ahmad Fagam)