Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sake duba tsarin yadda ake amsar kudaden shiga a manyan hukumomi masu samar da kudaden shiga.
- Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Manyan Makarantu Na Tsawon Shekaru 7
- Aikin Hakar Kwal Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Zamani Ya Fara Wuce 50% a Kasar Sin
Wadannan hukumomin sun hada da Hukumar tattara harajin cikin gida ta tarayya (FIRS), Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC), Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NIMASA), da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC).
Umarnin, wanda aka bayar a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka yi ranar Laraba a Abuja, na da nufin inganta samarwa masu biyan haraji rarar kudi, domin inganta walwala da kuma bude hanyoyin ci gaban tattalin arziki.
Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai.
Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban tattalin arzikin kasa a baya, amma a yanzu, za su karfafa kwarin gwiwar masu zuba jari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp